ADMINS KU JI TSORON ALLAH 3


*ADMINS KUJI TSORON ALLAH!!! 03*

*RADDI ZUWAGA DR. HAFIZU MOHD SHUWAKI*

*(USTAZU MAI ZANEN NONUWA)*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+237665087032
.
.
Yau 17/ 11/ 1441 wanda yayi dai-dai da 08/ 07/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka, jama'a wannan lekca ce wacce take raddi ne ga wani bawan Allah mai suna *DR. HAFIZU MOHD SHUWAKI*. Jama'a wannan mutumin yana cutar da matan aure a social media har ma da yanmata, watakila kunsan shi, watakila kuna cikin group dinshi, watakila kuna ganin rubutunsa. Shi dai wannan mutumin malami ne shi a social media, babu shakka yanada iliminsa dai-dai gwardo, amma baya amfani da iliminsa. A group dinsa yana tara matan mutane har da yanmata sai ya dinga binsu private chart yana musu maganar banza, daga cikin iskancin da yake koyawa yan group dinsa shine ya tura musu hotunan zanen nonuwa, bayan ya turamusu sai yace kowa ta fadi yanda takeson nononta ta koma, idan kuwa suka za6i wacce suke so, tho shi kuma sai yace su dauki nonuwansu su turamishi ya ga girmansu. Kuma na rantse da Allah haka wasu suke daukan nonuwansu suna turamishi yana jindadi, sai ya fake da cewa zai iya maidasu irin wanda suka zaba. Dan Allah wannan wane irin shaidani ne? Kunga kai tsaye wannan mutumin shaidani ne, kuma dukkan wadanda suke turamusu hotunan nonuwansu suma jahilai ne, domin nasan yawancin su rashin ilimi ne yasa suke haka, dayake su kuma sunji yace malami ne shi, tho shine sai su cigaba iskancin su tunda sun samu dama._

_Tho a karkashin haka insha Allah zan turomuku da lambobin da yake using dashi a rubutunsa, don kuyi blocking dinsa. Wallahi mata idan bakuyi a hankali ba WhatsApp zata kai ku wutar jahannama, wai wane irin rashin hankali ne ko ince jahilci da zai sa ku dinga daukan hotunan nonuwanku kuna turawa wani gardi? Wallahi zaki shiga wuta indai baki tuba ba, shikenan yanzu kin zama yar iska? Kin zama jahila wacce batada ilimin addini, batada ilimin zamani, batada ilimin rayuwa? Bakida hankalin da zaki iya tantance shaidani da ustazu? Meyesa kuka bari aka rainaku? Kuma na rantse da Allah yawancin masu haka matan aure ne sukafi yawa, wasu sunada 'ya'ya, saboda kana shiga group din ma zakaga ganinsu Ummu kaza, Ummu kaza, amma saboda an riga an jahiltar dasu basuda hankali, basuda tunani._

_A karkashin wannan bayanin zan baku shawara samari matasa har ma da maigidanci da kusani matan nan fah yawancinsu sun riga sun lalace dayawa, sun riga an lalata su a social media, sun riga sun zama tantirai karuwai dayawa, wanda kuma ba lallai bane kagane su ba, domin wasu zasu nuna maka Ustaziya ce, amma wallahi karuwa ce sakat, saboda haka kada ka yarda ka auri mace bakayi bincike akanta ba, wallahi idan ka tashi aure sai kayi da gaske, ka tashi tsaye ka tsanata bincike sossai akansu, kada ku bari wani banzan mutum ya baku fatawar cewa yawan bincike yana kawo matsala, tho karya yakeyi baya so kasan wacce zaka aura ne, Dole ka bincika suwaye kawayenta? Suwaye malamanta? Suwaye iyayenta? Suwaye abokanta? Ina da ina tafi zuwa? Wane irin groups take dasu a waya? Wallahi sai kayi bincike sossai. Domin idan ka kuskura ka dauko yar duniya, na rantse da Allah ka watsa gidanka, ka watsa 'ya'yanka. Domin kana fita aiki zata kawo kwarto a dakin ka yana iskancin da ita. Mata basuda kunya basuda tsoron Allah, domin binda yawancin mata sukeyi kenan._

_Yawancin wadannan matan nan ko, tho an fi lalata dasu ta hanyar waya, a waya zasuyi iskancin su kai kana can kana kwance a daki. Saboda haka duk wani magidanci kada ku yarda matayenku su kai karfe 10 na dare suna chatting da waya, kun anshi wayarsu, domin yawancin masu wannan lalatar sunada aurensu, domin mafi yawancinsu masu aure ne wallahi._

_Mata kuji tsoron Allah, mata kuji tsoron Allah, mata kuji tsoron Allah. Wallahi akwai ranar da zaki raina kanki, kina iskancinki kina jindadi ko? Tho Bismillah ki cigaba tunda baki da hankali, amma kisani zaki ci ubanki idan kika shiga kabari, kuma zaki shiga wuta idan kikaje lahira wallahi. Kuma wannan 6arnar yan film sunfi bada gudummawa sossai akanta wallahi, da kuma kananun Yan iskan nan irinsu *MUNEERAT ABDUSSALAM (UWAR LUMANCY), da ZAINAB UKWU, da FAUZIYA* da dai saura irin yan iskan nan masu cewa suna koyar da sex education, domin suna kwaikwaiyonsu ne, domin suna samun labari yadda yan film suke samun kudi ta hanyar iskancin su a hotels, tho shine su ma suke kwaikwaiyonsu. Shiyasa zakaga matan aure har hotel suke zuwa su hadu da katon gardi ayi lalata da sh an biyasu. Duk wacce take da ja akan wannan maganar, tho Allah ya tsinemata idan bata fito ta karesu ba._

_Ita *MUNEERAT ABDUSSALAM* dama kowa ya santa cikakkiyar zindikiya ce, kuma tanada tabun hankali sossai ga duk wanda yasanta. Saboda haka insha Allah duk sai mun biku daya bayan daya mun 6ata wannan muguwar ayyukan da kuke koyawa yaranmu, kuke koyawa iyayenmu mata. Saboda rashin kunya irin na yaran nan sai kaga sun fito suna bayani yadda ake kwanciya, in banda iskanci irin nasu, su basuyi aure ba, su basuje islamiyya ba, tho ina ruwan yar tasha da wa'azi? Ina ruwan zindikiya da wa'azi? Amma dayake su ma matanmu basuda tunani sai suma suka biye musu. Ya Allah muna rokonka wadannan iskan yaran nan idan masu shiryuwa ne, ya Allah ka shiryesu, idan kuwa basuda rabon shirya, ya Allah ka kare 'ya'yanmu, kannanmu da iyayenmu daga sharrinsu. Ya Allah ka tarwatsu duka su zamo tarihi a social media._

_Zan dakata anan a lekca ta gaba zamuyi raddi zuwa ga wani zindinkin admin shima, domin shi 6arnarsa yafi na me zanen nonuwan mata. Kuma itama Muneerat Abdussalam zamu dawo kanta insha Allah._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)