*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Alamomin Hakikanin Jinin Haila_*
Yana da kyau mace ta iya gane hakikanin alamar jinin haila, da haka ne zata iya babbace tsakanin jinin haila da jinin ciwo.
Da haka za ta samu kwanciyar hankali kuma tayi ibada a cikin tsarki.
*_Ga alamomin kamar haka;_*
* Jinin haila jini ne daskarere yana tunkuda ko ace mai kauri
* Jinin haila baki ne ba ja ba, ya saba da jini na hakika
* Jinin haila yana hamami ko ace wari
Wadannan su ne alamomin jinin haila sai dai a wani lokacin ana samun sabani daga wani yanayin zuwa wani yanayin.
Duk lokacin da ya saba matukar yana cikin kwanakin haila ne to hukuncin jinin haila ya haukanshi.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*