HANYAR DA ZA KI GYARA JIKINKI


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Hanyar Da Zaki Gyara Jikinki, laushi da Haske_*

Yar uwa gyara jiki wani abu ne mai mahimmanci ga mace domin yana haifar mata da hasken jiki da kuma gamshi a jikinta don nishadantar da abokin zama.

Abubuwan da zaki nema sune kamar haka;

* Sabulun salo
* Sabulun ghana
* Lemun tsami
* Kur kur
*Bayani;* Sai ki hada sabulan wuri guda da kur kur din sai ki juya kadan sai ki dauko lemun tsaminki sai ki matsa a ciki kar yai yawa sai ki cigaba da juyawa har sai ya hade sai ki dunga wanka da shi, bayan kin fito wanka sai ki sami man ridi ki dunga shafawa, da yardan Allah zaki ga yadda zai gyara miki jiki, fatanki ta rinka sheki da sulbi.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)