LABARIN YUSUF DA BALA

Yusufu da Bala

Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wasu yara su biyu; Yusufu da Bala, wata rana ana biki a gidansu, sai aka aike su su je daji su yanko yakuwar miya. A kan hanyarsu ta tafiya sai suka ci karo da wani ƙaton zakara da ganga rataye a wuyansa. Sai zakaran ya tambaye su, “Yara-yara ina za ku je ne?”, sai suka ce da shi, “Za mu je mu yanko yakuwa ne”, sai ya ce, “Na yi muku ɗan kiɗa ku ji?”, sai suka ce, “e”, sai ya fara”.

Tamagungun-tamagungun muƙut sai ya haɗiye su.

Can a gidansu yaran kuwa, aka ga yara sun jima basu dawo ba, saboda haka sai iyayensu mata suka bisu, sai suma suka haɗu da wannan zakara. Da zakara ya gansu kawai sai ya fara waƙa:

Zakara: Ku-ku-ku ina za ku, tarmanamana
Mata: Neman ‘ya’yanmu za mu tarmanamana
Zakara: Su ‘ya’yan ina za su, tarmanamana
Mata: Ɗiban yakuwa za su, tarmanamana
Zakara: Ɗiban yakuwar mene, tarmanamana
Mata: Ɗiban yakuwar taushe, tarmanamana
Zakara: In yi muku ɗan kiɗa ku ji? Tamagun-tamagun, muƙut sai ya haɗiye matan suma.

Da jama’ar gari suka ga shiru, yara basu dawo ba, haka nan ma iyayensu mata, sai dukkan mutanen garin har da sarkinsu suka fita neman su. Da suka haɗu da wannan zakara suma duk sai ya haɗiye su.

Can sai ga wani mutum shi kaɗai ya fito daga wani garin, yana kan hanyarsa ta tafiya, sai ya haɗu da wannan zakara, da suka haɗu, sai zakara ya yi yunƙurin haɗiye wannan mutumi, bai gama haɗiye shi baki ɗaya ba, sai wannan mutumi ya hango waɗannan jama’a da wannan zakara ya haɗiye, ganin haka dama hannun mutumin nan akwai wuƙa, saboda haka sai ya ƙara dagewa har sai da ya farka cikin wannan zakara ya faɗi matacce, sauran jama’a kuma kowa ya fito ya kama gabansa.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya

 

Post a Comment (0)