🚫 SUN YAUDAREKA DA CEWA KAI YARO NE KARAMI.
Daga malama Aisha isah.
Ku kyaleshi yaro ne karami.
Ku saukaka masa yaro ne karami.
Ku rabu dashi yaro ne karami
Yana saba umurnin 'iyayensa, ya daga musu sauti, amma mutane suce a kyaleshi yaro ne karami.‼
Yana yawo da abokan banza, yaki dawowa gida sai cikin dare, idan kuma za'a hukuntashi mutane suce matashi ne zai daina yaro ne karami.‼
Baya sallah, yana karya sannan yana daukan kayan mahaifiyarsa ba tambaya, dukda haka sai ace arabu dashi yaro ne karami.‼
Haka muka lalace da daukan kura_kuran yarammu dana abokan arzikimmu a matsayin yarinta, Kalmar yarintan kuma 'ita taci gaba da basu lasisin yin abinda suka gadama.
A fayyace yake, wannan yaudara ce babba, ya jama'a musani shifa farawar shekarun samartaka shine farkon lokacin daura nauye nauyen shari'a ga yarammu, lokacine da mala'iku suke fara rubuta abinda suke aikatawa kuma za'a musu hisabi akansu.
Kenan kuwa wadannan shekaru shekaru ne na hankali da nutsuwa da shiryuwa ba shekaru bane na wawanci, sakarci da wauta.
Kusani ya jama'a ansamu matasa masu kananun shekaru da suka taka rawar gani a tarihin musulunci‼
Wanda ya bude kasar andalus matashi ne, sunansa Abdurrahman Annasir shekarunsa 21.
Wanda yabude kasdandiyniyya matashi ne, shekarunsa 22.
Shugaban rundinar sojojin musulmi, kuma aciki akwai manyan sahabbai kamar abubakar da umar matashi ne, usamatu bn zaid shekarunsa 18.
Wanda yabude kasar sind Muhammad Alkasim assaqafiy matashi ne, shekarunsa 17.
Farkon wanda yafara harba kibiya don daukaka kalmar Allah matashi ne, sahabi sa'adu bn abiy waqqass r.a.
Wanda yabude gidansa ga manzo s.a.w da sahabbansa a makka matashi ne sunansa arqam bn abi arqam shekarunsa 16.
Me karamci ne acikin larabawa ko acikin musulunci dalhatu bn ubaidullah, matashi ne shekarunsa 16 kuma ana masa laqabi da mataimakin manzo s.a.w.
Farkon wanda yafara zare takobi don daukaka Kalmar Allah matashi ne, zubairu bnl awwam shekarunsa 15.
Matasammu na yanzu saidai wanda Allah yayima rahama, shekaru 25 haka za'a dinga cigaba da alakantasu da yarinta ko kuruciya.
Wannan yakin kwakwalwa ne ‼
Nauye nauye ne daya rataya akan iyaye maza da mata.
Ya Allah kamaida matasa da yammata da dukkan musulmi gareka mayarwa mai kyau.