MAHIMMANCIN TAIMAKON MABUKATA MUSAMMAN A WANNAN YANAYI NA CUTAR CORONA
Babu shakka a yau al'umma tana rayuwa cikin tsanani da mawuyacin hali tun lokacinda Allah ya jarrabi duniya da cutar Corona wanda wannan yasa akwai bukatar wadanda keda rufin asiri suyi amfani da dama wajen taimakawa da tausayawa mabukata tareda yaye musu damuwarsu da halin kuncin dake suke ciki.
Ayoyi da hadisai masu tarin yawa sunzo don nuna mahimmancin taimakon masu rauni musamman alokacin tsananin bukata kuma siffa ce daga cikin siffofin mummunai.
Daga cikin kyawawan dabi'un Manzon Allah (SAW) tun kafin aikoshi amatsayin Annabi akwai sada zumunta da taimakon mabukata da sauran masu rauni.
Haka Manzon Allah ya yabi Al-ash'ariyyeen wadanda idan abincin iyalinsu yayi karanci sai kowanensu ya kawo abinda yake dashi a tara wuri daya a raba daidai.
Kazalika Manzon Allah yace duk wanda ya yayema Musulmi wata damuwa daga cikin damuwowin duniya Allah zai yaye mishi damuwar lahira.
Kasancewar bana ba za'aje aikin hajji ba dama ta samu ga mawadata suyi amfani da dukiyar dasuke biyanma kansu da sauran mutane kujerun aikin hajji su taimakama talakawa da miskinai domin amfanin jama'a dayawa yafi amfanin mutane kadan.
Don haka kowa yaga abinda yake iyayi wajen taimakawa masu rauni musamman gashi muna fuskantar kwanaki goma na farkon Zhul hijja wadanda sune ranaku mafi falala da daraja acikin ranakun duniya.
Kadan daga cikin fasarar khudubar da Sheikh Sa'eed Aliyy Maikwano Gusau ya gabatar.