PRIYANKA CHOPRA
Gaisheki Jaruma Priyanka
Babu kokwanto wuyarki ta isa yanka
Giwa kike kin fi gaban karnuka
Daddawa kike kece me gyara miyar kuka
Hasken rana kike abin biΙa gun shuka
Alfaharin Bollywood kike jaruma Priyanka
Ke mata suke shayi yau ba ki da tamka
Amaryar Ιan Jonas yau gare ki nake baituka.
Ke ce abin girmamawar mutanen kudu
Ke ce abar alfaharin mutanen arewa
Ke ce abar son jama'ar gabasawa
Ke ce mai sanyaya ruhin jama'ar yammawa
Sarauniyar Bollywood babu mai tankawa
In ta fito dole mata su yiyo rusunawa
Ko ba sa so dole su yo gaisuwar girmamawa
Jinjinar ban girma nake a gareki Priyanka.
Kyakkywa ce ita jaruma Priyanka
Attajira ce ita jaruma Priyanka
Shahararriya ce ita jaruma Priyanka
Kuma gwana ce ita jaruma Priyanka
Ta riga ta karΙu a Indiya Priyanka
Ta yi Ζauri na suna a Amurka
Ko ba ka sonta ka san ta Ζware Priyanka
Hakan ya sa a yau nake waΖe wacce ba ta da tamka.
Ni ne Jamilun nan na Kaduna
Al-katib da ke a Kaduna
Salon aiki ne yau na nuna
A cikin saΖon wake daga guna.
©️✍π»
Jamilu Abdurrahman
+2348185819176
