TAMBAYA TA 78


*Tambaya:*


Assalamou alaykum wrhmtllh 
Malam brk d wrhk 
Ya aiki?
Malam macece mijinta yake neman aure ,ama kuma yanata zuwa yana batata a wurin budurwar tasa.tasha ji da kunnenta yana hada mata karya akan abinda batayiba.Malam zata iya rokon Allah akan zalincin karyar da ake mata akan Allah ya lalata lamarin auren nasu?
Jxkllh khair
.

*Amsa:*


Wa'alaikumussalamu Warahmatullah. 

Allαн(ﷻ) Yana cewa:

*”يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ.“*

Ma'ana: *“Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nemi taimako da haƙuri da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri.”* [Al-Qur'an 2:153]

'Yar uwata mai daraja! Ina yi maki wasici da ki ji tsoron Allah, kada ki biye wa wasi-wasin shaiďan da 'yan maganganu da za su yi ta kai kawo daga bakin mutane a lokacin da mijinki zai qara aure. 

Wasu za su zo maki da labarin da bai faru ba su faďi maki kawai don su ga sun kore zaman lafiya tsakaninki da mijinki, ki tada hankalinki ki dinga sanya kanki a damuwa, da burin baqanta wa mijinki, hakan ba zai qare ki da komai ba illa ya saka maki ciwon zuciya, rikicewar tunani da mutuwar jiki. Kuma ba zai sa ya fasa qaro auren ba, hakan ma zai qara masa qarfin gwiwa ne don zai yi tunanin idan ya qaro auren zai samu kwanciyar hankali a wajen amaryar. 

Idan kuwa kin ji lokacin da yake kalamai na 6atanci a kan ki. To ki danne zuciyarki kada ki nuna damuwarki, nuna damuwarki shi zai sa ya ji daďi a ransa domin dama hakan yake buqata. 

Lallai ne akwai wani shaiďani da yake tare da shi, domin yana daga cikin manyan burin shaiďanu su ga sun farraqa tsakanin ma'aurata, ko su hana su zaman lafiya ko su hana auren da ake so a yi. 

A lokacin da za su dinga zuga shi a kan ya dinga yin abubuwan da za su 6ata maki rai, ke kuma za su dinga cusa maki zummar ďaukar fansa a kan abin da yake yi maki. Don haka ki yi kokari ki ci gaba da addu'ar Allah Ya tabbatar da abin da zai zama mafi alkhairi. 

_🗯️A gaskiya babu sakaran namiji kamar wanda zai dinga yin kalaman 6atanci game da uwar 'ya'yansa a wajen abokai, budurwa ko bazawararsa._

_🗯️Ku kuma mata ku yi taka tsan-tsan, kada ki sake ki auri wanda zai dinga zuwa yana kushe matarsa idan ya zo hira wajenki, ko ya dinga buďe maki sirrikanta. Domin wallahi idan kika aure shi wata rana sirrinki zai ďauka ya kai wa wata a waje. Domin kowanne mutum yana da abubuwan da ya dace su faku daga ilimin mutane, wato su zama sirri tsakanin ma'aurata._

Ina rokon Allah Ya ganar da mijinki ya daina abin da yake yi. Ba laifi ki yi masa nasiha ya ji tsoron Allah Ya daina. 

Domin ko da kin kai qararsa wajen iyayensa ba lallai ne su gasgata ki ba, za su yi zargin kishine ya sa kika zo ki yi masa qarya. 


Allah Ya sa mu dace, Ya tabbatar da abin da ya fi alkhairi a rayuwarmu. 

Wallahu A'lamu. 
.
.
Daga:
*🕌Zauren Irshadul Ummah.*

Za ku iya bibiyar mu ta kafofin sadarwa kamar haka:

*WhatsApp:*
+2348166650256.

Ko ka ziyarci shafinmu na 
*Telegram:* t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)