WAƘAR KUKAN SO
RUBUTAWA: Jamilu Abdurrahman
Rerawa: Lalo
Shekara: Mayu, 2020
Kukan so nake yi rabuwa ta mini rauni, mai sona ta guje ni wayyo.
Soyayya kun sani ta na da daɗi,
Ɗanɗanonta kun sani yana fa da garɗi,
Yanayinta in kana ciki sam bai da misali,
Barin ace ka samu ɗiya mai kyawun hali,
Tabbas rayuwa ta yi daɗi sai dai farinciki.
Mai Sona tana da kyawun hali ba muni,
Ga kyan suffa za ta birge ka in ka ganta,
Kwalliyarta ko Indiya ai sai an tona,
Muryarta kamar ta tsuntsuwa mai waƙa,
Shekaru mun ka ɗauka muna soyayya.
Na nemi izini kuma dama har an bani,
Daga baya aka janye damar da aka bani,
Wai karatu za ta yi shi ya sa aka hanani,
Na yi mita na yi mita amma aka share ni,
Ashe gulma ce aka shirya a gareni.
Da ni da ita juna mun amincewa,
Hakan yasa ruɗin zuciya mu ke kaucewa,
Tafiyar mu tana nan amma sam ba riba,
Babu halin in ganta bare ma mu yi magana,
Daga ƙarshe ta bayyana mini dukkan makircin.
Wani laifi ne da akai na kisa aka ce ni ne,
Bayan bayani ya bayyana cewa ba ni ne ba,
Magulmata su ka kai tsegumi gidansu,
Shi yasa ashe izinin ma wai aka janye,
Kun ji halin Magulmata akan soyayya.
Kuma wai sai an ka ce mata ɗan iska ne ni,
Wasu ma sai suka ce mata wai kwarto ne ni,
Gulma kullum ake kai mata don a kushe ni,
Har dai ta ɗauka ta kore ni babu dalili,
Ga shi yanzu ina kuka a cikin baƙin ciki.
Soyayyarta a zuciyata na nan ba canji,
Begenta nake dare da rana ba ƙaƙƙautawa,
Rabbana Ka sa ta gane ta fahimce ni,
MU dawo kamar da cikin soyayya,
Mu Ba maƙiyanmu kunya a cikin soyayya.