YADDA AKE HAƊA BAƘAR HUMRA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hada Bakar Humra_*

Yar uwa yana da kyau ace kina hada kayan kamshi ta yadda zaki kasance koda yaushe dakinki, jikinki da kayanki a cikin kamshi.

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Mahala
* Farco, hawi
* Turaren sandal
* Madarar turare kamar kala uku
* Turaren bahur ko aladin
*Bayani;* Zaki dake mahala ko aladin ki dauko mahala da hawi da farco ki tankade su ki hade su guri guda sai ki dauko wadannan turarukan ki hada wuri guda sai ki kawo dakakkun kayan ki zuba akansu zaki ga sunyi kasa, shine yake sasu tsamawa amma farco sai kin wanke kin soya idan ba haka ba dakakke ba ne kika samu.
 
Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)