ZIKIRIN SAMUN GAFARAR ZUNUBAI


#ZIKIRIN SAMUN GAFARAR ZUNUBAI 

Daga bn Haarithata رضـي الله عنه, Lallai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yace:-
(Duk wanda yace 
*_أستَغـفرُ اللَّهَ الَّـذي لا إلَـهَ إلَّا هـوَ الحـيَّ القيُّـومَ، وأتـوبُ إليـهِ_*
Astaghfirul-lahal-lazee la ilaha illa huwal-hayyul-qayyoomu wa-atoobu ilayh. 
*An gafarata masa zunubansa ko da ya gudu ne a wajen yaƙi)*
 @صحيح أبي داود للألباني (١٥١٧) 

✍🏻الحافظ النٌـوُوي رَحِـمَهُ الله:
Yana cewa:-
*"Da mutum zai maimaita zunubi har sau ɗari ko fiye da haka, ko ya maimaita sau dubu ko fiye da dubu, kuma yayi tuba a duk lokacin da yayi wannan zunubin, to Allah ya karbi tubansa ko wannan zunubin nasa ya fadi babu shi, da kuma zai tuba daga dukkan zunubansa gaba daya yayi tuba daya, to hakika Shima tubansa yayi kuma zunubansa sun fadi daga kansa"*
@شـرح صحيح مـسلم (17/ 75)

•العلامة ابن عثيمين عليه رحمات رب العالمين - :
Yana cewa:-
*_Ya kai Ɗan uwana mai albarka, ina maka wasiyya akan ka yawaita yin ISTIGHFARI da faɗar ALLAHUMMAGH FIRLI, ALLAHUMMAR HAMNEE, ASTAGHFIRULLAH WA'A TUBU ILAIHI_*

Ka yawaita Istighfari da nau'ikansa a kowane lokaci dan ka dace da lokacin amsawa, da zaran an dace da lokacin amsawa to an gafarata maka zunubanka gaba daya.
@شرح رياض الصالحين (٦ / ٧١٦) 】
‏‌‏═════ ❁✿❁ ══════


      Allah ne Mafi
Post a Comment (0)