BARKA SALMAN KHAN
A yau ne jarumi Salman Khan yake cika shekaru 32 da shigowa masana'antar shirya fina-finan Indiya. To sanin kowa ne dai cewa ni ba fan ɗin Salman Khan bane, amma ina son shi saboda shi ɗan uwana ne musulmi, wannan kuwa ya isa komai. Bugu da ƙari, jarumi Salman Khan gwani ne da duniya ma ta aminta da gwanintarsa, shahararre ne wanda duniya ta yarda da shahararsa kuma ya kai matsayinta da ko ba a so dole a girmamashi in dai a harkar fim ne. Don haka ina taya shi murnar zagayowar wannan rana, haƙiƙa salman abun alfahari ne a wajenmu. Ko da yake ban aminta da mafi yawancin tsare-tsaren rayuwarsa ba, na aminta da nagartar aikinsa. Ko da yake yana da matsaloli da dama a rayuwarsa, nima ai ina da nawa mas'alolin. Ko da yake yana aikata kura-kurai da dama a raywarsa, nima ai ina aikata kura-kuran. In kuwa har haka ne, to kowa ya ji da nashi, sai a zauna lafiya.
Fatan alheri wa salman da masoyansa, Allah ya ƙara masa ƙarfin imani, Allah ya ƙara gyara masa al'amuransa, ya bashi mata ta gari, ya bashi sa'a akan fina-finansa na gaba kuma ya kare shi daga sharrin maƙiya. Nagode
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
Haimanraees@gmail.com