FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA


FASSARAR FINA-FINAN INDIYA ZUWA HARSHEN HAUSA

An jima da fara kallon fina-finan Indiya a ƙasar Hausa wanda shi ne tubalin da ya gina masana'antar fina-finan arewacin Nijeriya da aka fi sani da Kannywood. To amma, da shekaru takwas zuwa goma da suka gabata izuwa yanzu, masana'antun fina-finan Indiya (Musamman Bollywood da Tollywood) sun ƙara samun mabiya a ƙasar Hausa fiye da da, wannan kuwa ya biyo bayan fassara fina-finansu ne da aka fara yi a cikin harshen Hausa.

Duk cewa an ɗauki tsawon shekaru kusan 50 ana kallon fina-finan Indiya a ƙasar Hausa, mafi yawancin makallatan suna wannan kallo ne ba tare da sanin ko da kalma guda ta harshen Hindi ba. Yayin da wasu kuma ke amfani "Subtitles" wajen fahimtar saƙon da fina-finan ke ɗauke da su. To amma duk da wannan ƙarancin fahimtar yare da ake samu, hakan bai hana a ci gaba da kallon fina-finan ba, musamman irin yadda mafi yawancin saƙonnin fina-finan ke kamanceceniya da halaye da kuma ɗabi'un muatenen ƙasar Hausa. A hankali kuma sai aka fara samun zaƙaƙuran matasa a ƙasar Hausa waɗanda sha'awar fina-finan ta sa suka fara bibiyar al'amuran yau da kullum da suka shafi masana'antun fina-finan ƙasar Indiya, wannan shi ne ya haifar da samuwar nagartattu kuma Ingantattun bayanai da suka shafi jarumai, fina-finai da sauran al'amuran da suka jiɓincin harkar baki ɗaya.

Abun bai tsaya a nan ba, domin kuwa ba tare da wani jinkiri ba sai aka fara samun masu nazartar yaren Hindi tare kuma da ƙoƙarin ganin sun koyar da wasu wannan yare. Wannan ya haifar da samuwar ƙungiyoyin da suke ɗabbaƙa al'adu da kuma sauran al'amuran da suka shafi masana'antun fina-finan Indiya. Daga nan sai taruka suka fara samuwa da kuma bukukuwan sallah inda akan haɗu a yi zumunci a yi nishaɗi tare da ƙarawa juna sani dangane da harkar baki ɗaya. A dalilin haka an samu abota da dama wasu ma har ta kai su ga yin aure. Samuwar masu gabatar da shirye-shiryen da suka jiɓinci fina-finan Indiya a gidajen Talabijin da kuma gidajen Rediyo a arewacin Nijeriya sai ya zama ya ƙara hura wutar soyayyar da ake yi wa jarumai da kuma fina-finan Indiya a yankin ƙasar Hausa. Wannan ya sa aka ƙara samun haɗuwar kai da kuma yaɗuwar sabbin ƙungiyoyi majiɓantan harkar.

Zuwan shafukan sada zumunta irin su Facebook, Twitter da kuma Whatsapp sai ya bawa masu sha'awar wannan harka ta fina-finan Indiya damar haɗuwa da juna kai tsaye tare kuma da samun bayanai akan jarumansu da kuma sauran al'amuran da suka shafe su kai tsaye. A yayin da duk wannan ci gaba ke samuwa kada mai karatu ya manta cewa; masoyan wannan harkar ne ke ci gaba da kawo waɗannan ci gaba wanda hakan shi kuma ya haifar da ƙarin mabiya.

Ana cikin wannan ne kwatsam kuma sai ga harkar fassarar fina-finai izuwa harshen Hausa ta samu a cikin harshen Hausa kuma daga Hausawa 'yan asalin yankin ƙasar Hausa. Hakan yasa nan take mabiya wannan harka ta Indiya suka ninku daga biyar zuwa talatin cikin dare ɗaya, domin kuwa da yawansu suna son fina-finan ko da basa fahimtar abin da ake cewa yanzu kuwa da suka fara fahimtar saƙon, sai soyayyar da suke yi wa fina-finan ta ƙaru. Saboda ƙaruwa da fina-finan Indiya suka samu a fannin masoya da kuma masu bibiyar harkar, sai da ya zamana masana'antar fina-finan Kannywood da kanta ta girgiza. Domin kuwa hakan ya jawo samun ƙarancin kasuwancin fina-finansu a kasuwa, har sai da ta kai cewa masu sarin fina-finan sun gwammace su sari fina-finan fassara akan su sari fina-finan da Hausawan suka shirya.


Zan ci gaba in sha Allah.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

मियां भाई की डेटिंग 
Post a Comment (0)