TAMBAƊAƊIYA


TAMBAƊAƊIYA

• Har yanzu ina nan ina zance kan Mujiya. 
• Kangana ko kuce Firgitacciya. 
• Mai sukar Addininmu ita ce la'ananniya. 
• Ga ta 'yar ƙyamas kama an ɗaura zane ga Muciya. 
• Kin yi asara yar bayan gari Makauniya. 

• Maras hankali kai kuce mata Mahaukaciya. 
• 'Yar bala'i ku kira ta Masifaffiya.
• Ja'ira mai ja'irci 'yar jagaliya.
• Allah ya watsa lamarinki ki zamo Tambaɗaɗɗiya. 
• 'Yar maye mai shisshigi Makakkiya. 

• Shagiɗaɗɗiya mara kunya Karkatacciya. 
• Sai zare ido kamar ana yi wa Mujiya tsargiya. 
• Jemammiya, 'yar bishiya Lanƙwasashiya. 
• Allahu kasa wanga baiwa taka ta gane gaskiya. 
• Ta shiryu ta dawo hanyar Muhammadu mai son gaskiya. 

• Ta daina ƙwafa da makirci ta gane gaskiya. 
• In kuma ba ta da rabo ka sa ta zamo Wulaƙantacciya. 
• A koma gudun ta tun da ta zamo Annamimiya. 
• A wayi gari ta yo mushe ta zamo Sheƙaƙƙiya. 
• Busashiya, mara tsari Wahalalliya. 

• Jamilu ne na Kaduna ke waƙar raddi a gurin Watsatstsiya. 
• Ɗan Abdurrahman na Gadan nan mai bawa musulunci Kariya. 
• Makafcin zamani mai rattabe da ƙafiya. 
• jariri marubuta, neman ƙarin sani bai ɗaya 
• Ina muku sallama, Allah ya ƙare mu da lafiya. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com

Post a Comment (0)