FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN KICK
Shekarar Fita - 2014
Fassarawa - Jamilu Abdurrahman
• Pehda toh main bhi sharif hua tha ... par sharafat se apni kabhi nahi bani
Nima kaina da gaskiya aka haife ni... Amma na kasa ci gaba da rayuwa da gaskiyar.
Nawazuddin Siddiqui
• Mere bare mein itna mat sochna ... dil mein aata hoon ... samajh mein nahi
Kada ki yi tunani a kaina... A cikin zuciya nake... Amma ina da wuyar fahimta.
Salman Khan
• Rishtey ko mazboot hona chahiye ... majboor nahi
Kamata ya yi ace alaƙa ta zama abu mai ƙarfi... Ba abinda za a kasa taimakawa ba.
Salman Khan
• Ek ek paisa gin lena thook laga ke ... yeh ho na ho hum toh traditional kaminey log hai
Count every note with your
Ka ƙirga kuɗin da yawu... Ta yiwu shi ba haka yake ba, amma mu 'yan iskan gargajiya ne.
Nawazuddin Siddiqui
• Machli chahe kitni bhi tezz ho ... ek baar kaante mein phas jaye toh kilo ke bhav bikti hai
Komai hanzarin kifi... Da zarar ya shiga ƙugiya, to a kilo za a siyar da shi.
Randeep Hooda
• Izzat, zillat, shohrat aur maut ... upar waale ke haath mein hai
Daraja, tozarci, arziƙi da mutuwa... Duk a hannun ubangiji suke.
Mithun Chakraborty
• Aap devil ke peeche, devil aapke peeche ... too much fun
Kana Bayan shaiɗan, shaiɗan na bayanka... Nishaɗin ya yawaita.
Salman Khan
• Mujhse joh dushmani modh leta hai ... uspe uparwaala reham toh kar deta hai, magar main nahi
Wanda duk ya zama maƙiyina... Ubangiji na iya yafe masa... Amma ba ni ba.
Salman Khan
• Koi umeed bar nahi aati, koi soorat nazar nahi aati ... maut toh ek din moiyan hai, neend raat bhar kyun nahi aati ... pehle aati thi haal-e-dil pe hassi, ab kisi baat pe nahi aati
Babu wata fata da za a yi, babu kuma wani sulhu da za a samu... Mutuwa ƙaddara ce da sai ta zo watarana,amma me ya sa na kasa bacci tsawon dare... Da fari dariya nake yi akan damuwar zuciyata, amma yanzu kuma na kasa dariya akan komai.
Nawazuddin Siddiqui
• Main case aur face kabhi nahi bhoolta hoon
Ba na manta taƙaddama da kuma fuska.
Randeep Hooda
• Jisse zindagi ki parvah hoti hai ... maa kasam maarne ka mazaa us hi ko aata hai
Irin masu damuwa da rayuwa ɗin nan ko... Na rantse da mahaifiyata kashe su akwai daɗi.
Nawazuddin Siddiqui
• Chehre par gussa, mann mein gaali ... goli bhi chalali ... phir bhi dono haath khali
Akwai fushi a fuskarka, tsinuwa kuma a cikin zuciyarka... Har ma ka harba harsashi... Amma duka hannayenka fayau suke.
Salman Khan
• Meri vardi pe medal bahut lage hai ... par daag sirf ek
Akwai lambobin girmamawa da yawa a jikin kakina... Da kuma datti guda ɗaya.
Randeep Hooda
• Dawai aur shaadi mein badi similarity hoti hai ... dono agar time pe na mile na, bahut mushkil ho jaati hai
Akwai babban kamanceceniya a tsakanin magani da kuma aure... Idan har ba ka same su akan lokaci ba, to za ka fuskanci gagarumar matsala.
Saurabh Shukla
• Woh jeena bhi koi jeena hai jis mein kick na ho
Rayuwar duk da babu nishaɗi a cikinta ba rayuwa bace.
Salman Khan
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com