*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 20```
.
HANNU DAYA BAYA DAUKAR JINKA
Haka Bahaushe yake cewa, alokacin da ka so fara wata sana'a ko aiki naka na kanka ko kasuwanci dole za ka buqaci mutanen da za su taimaka maka wurin cika burinsu, misali wani tsohon ma'aikacin banki da ya yi wani qwarqwaryan shago, ya dora wani makusancinsa don ya tafiyar masa da shi, ya kawo duk abinda ake buqata masamman na'urannan ta bankin tafi da gidanka, wannan abu ne mai kyau matuqa tunda makusancinsa yana samu da shi, sai dai duk abinda da mutum zai tsara matuqar zai nemi taimakon wasu to ya tabbatar wadanda suka dace ne za a saka a wurin.
.
Taimakon na kusa da kai wajibi ne, akwai halin ma da za ka kawo shi kusa don ya riqa ba ka bayanin duk abubuwan dake faruwa, amma dagewa cewa naka ne kawai za ka sanya a wuri matsala ce babba wace za ta iya ruguza maka shiri, sai in ya cancanta da matsayin, wasu kan yi sha'awar sanya 'yan uwansu makusanta a wararen sana'a da kasuwanci alhali 'yan uwan ba su cancanci wurin ba, a qarshe sai ka ga an qare da nadama, kodai dan uwan ya aikata ma-sha-a, ko ya yi sama-da-fadi da dukiyar wasu ko handama da babakere, duka dai munanan abubuwa ne, ko dan uwanka yana da takarda ka tabbatar ya zauna a wasu wuraren dake da alaqa da aikin, ya naqalci komai, kuma yana da alqawari.
.
BIYAYYA
Alqqwari a aiki da tattali da tanadi koyonsa ake yi kamar yadda ake koyon aikin kansa, galibin masu kukan cewa sun dauko 'yan uwansu sun cuce su za ka taras ba wata horarwa ta masamman da suka samu kafin su shiga sana'ar, ba su koyi yadda za su yi ta'amuli da dukiyar wani ba ko kadan, abinda suka sani kawai yanzu za su shiga kudin dan uwansu, shi ya sa nan da nan sai ka ga abin Allah-wadai ya faru, a qarshe kuma su haramta musu ci gaba da ma'amalla da su har abada, su ce bare ya fi dan uwa, alhali su suka yi kuskure tun farko.
.
DAIDAI RUWA DAIDAI QURJI
A duk lokacin da ka ce kai da abin hannunka kawai za ka yi harka kana da matsala, amma kimanin shekara 3-4 da suka gabata na taba ganin wani malami yana bayanin cewa kar mutum ya taba karbar bashi a kan wata sana'a da zai fara, ya ririta abinda ke hannunsa kawai, na ga kuma wadanda suka yi masa raddi da cewa kashi 75 cikin dari na wadanda suka ci nasara ba da dukiyar hannunsu suka yi aiki ba, masamman masu manyan ma'aikatu da masana'antu, to dai duk abinda mutum zai yi kar ya taba yarda ya sha ta fi ciki, dole a ci bashi amma wanda za a iya biya ba wahala, kamar wanda za a gyara wuri a qara jari da makamantansu.
.
KULA DA MATAIMAKA
Duk lokacin da mutum yake ganin cewa shi fa zai rayu ko shi kadai ne kuma ba ya buqatar taimakon kowa to akwai matsala babba, amma abu mafi girma a ciki shi ne son kai, wato ya kasance mutum komai shi kadai yake so ya kwashe ba ruwansa da kowa, in kana da wurin sana'a kar ka yarda a ce kanka da iyalanka kadai ka sani, yi qoqari a ce hatta mai yi maka gadi yana da matsayi a wurinka, kuma kana ba kowa haqqinsa yadda ya dace, ko kwana daya mutum ya yi ba ka gan shi ba tambayi inda yake, za a gaya masa cewa ka tambayi halin da yake ciki, in bai da lafiya ne kuma ba za ka iya zuwa duba shi ba saboda wani zarafi yi qoqari ka kira shi a waya, in kana da dan wani abin hasafi ka yi masa, in ka matso kusa da ma'aikatanka ba za ka taba ganin abinda zai dame ka ba, mutum yana son alkhairi koda kuwa ba yawa.
.
IN GORA TA CIKA BA TA QARA
Haka Hausawa suke cewa, in ka ga mutum yana ji da kansa kuma yana nuna isa da fankama a wurin sana'arsa to bai shirya aikin sosai ba, matso kusa da ma'aikatanka ka janyo su jiki, komai ku riqa yi tare, za ka ga duk abinda ya taso sun iya samun qarfin gwiwar da za su tuntube ka ko ku tattauna tare, kar ka zama kamar dodo kowa na tsoron ya yi magana da kai, a irin wannan matsayin abubuwa da yawa za su yi ta faruwa ba ka sani ba, yanzu an fara fahimtar amfanin haka, akwai wani mai neman gwamna da mai neman dan majalisa da na gani, alla-alla suke yi su ji an yi rasuwa ko taron biki ko suna a duk yankinsu ka gan su a wurin, mafi yawancin tarurrukan da suke halarta ba gayyatarsu ake yi ba, amma suna so ne a gan su a yaba da qoqarinsu a qarshe a zabe su, dan majalisan ya ci, mai neman gwamnan ya fadi, dukansu biyun dai sun dena abubuwan da suka fara, na ce da sun sani su ci gaba, don gabar ta fi baya yawa.
.
MAGANIN MATSALA
Wasu fa ba su san yadda za su magance matsalolinsu ba samsam, idan mutum ya yi kuskure a wurin aiki sai maigidansa ya yi masa kaca-kaca a gaban jama'a, wani lokacin ma ya kore shi, na ji wanda yake iya bakin qoqarinsa wajen tsare hanyar cin abincinsa, amma da ya yi kuskure daya, haka maigidan ya zazzage shi kuma ya kore shi, ko aure mutum yake yin kuskure wajen gyara shi ko tantama ba na yi zai sami matsala wajen zama da mace, a shekarun baya na yi hira da wani tsoho wanda yake ce min ya yi aure so goma sha biyar, amma mata biyu na san shi da su, na ji matar da aka ce masu zaman haya a gidanta ba sa yin shekara sun gudu, saboda rashin iya ma'amalla, na ga wani mai sana'a duk wanda ya zo koyon aiki wurinsa sai ya gudu, bai iya ma'amalla da su ba.
.
Na ga malamin jami'an da ya yi hatsari dalibansa suke addu'ar Allah ya qarisa shi a asibiti, suka ce ina ma ya mutu tun daga wurin hatsarin, na ga wanda wani mutum ya jawo shi don su yi sana'a tare, amma ya munana ma'amallarsa, ya mayar da wurin nasa shi kadai, a qarshe ya sallami wanda ya kawo shi, ba a jima ba lamarin nasa balbalce, dole mu riqa kyautata alaqarmu da masu yi mana aiki ko masu aiki a qarqashimmu ko dalibammu matuqar muna son ganin ci gaba a rayuwarmu.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```