*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 19```
.
DA KAYAN KAI AKE NA RATAYA
Akwai hikima mai girman gaske mutum ya fara tunanin yin wani abu a gefe nasa na kansa wanda zai taimake shi, in likita ne yana da kyamis, in babban malamin makaranta ne yana da wata 'yar makaranta a gefe koda kuwa ta lesson ce, in kanikanci kake yi a wurin wani maigidanka na tsawon lokaci ka sami wani dan wuri a qofar gidanka kana gyara wa maqwabta mashinansu, in kafinta ne ka fara gyara wa mata 'yan kujerunsu a cikin gida lokacin da ba za ka je wurin aiki ba, wannan shi ne wayewa, a duk lokacin da ka gama qwarewa ko ba a sallame ka ba za ka yi naka na kanka.
.
Akwai hikima mai girman gaske mutum ya fara tunanin cewa zai iya yin wani abu nasa na kansa, koda kuwa talaka ne kamar yadda muka lissafo bare wani babban ma'aikacin gwamnati mai aiki a wata babbar ma'aikatar tatse 'ya'yan bishiya, in mutum na samun kudi ya gane cewa in fa ya sauka daga muqaminsa kudinnan da yake samu sun gama shigowa kenan sai dai kuma shigewa, yanzu sai ya fara tunanin riqe su ta yadda ba za su qare ba, hakan kuma ba zai taba yuwuwa ba sai in ana qara yawansu, kenan ya fara tunanin yuwuwar yin wani abu da zai kawo kudin shiga.
.
Mafita ga wanda yake aiki a babban ma'aikatar katako ita ce: Me zai hana shi yin dan wani shago ya sami wanda zai riqa taimaka masa wajen tsarewa? Yanzu rashin aiki ya yi yawa, mutane na zaune ne babu aikin yi, kana fara neman mai taimako nan da nan za ka samu, sai ka koya masa aikin kamar yadda kake so ya yi, ka kawo kayan aiki masu kyau da nagarta, nan da nan za ka ga kana buqatar sama da mutum guda matuqar dai ka sami kayan aiki na zamani, ka inganta aikinka kuma ka qimanta shi a idonka, kana aiki a wani wuri kana fadada naka a hankali da abinda kake samu acan, kafin ka kai ga yadda za a ce ba a buqatarka a wurin aikinka kai kanka ka fara tunanin ya dace a ce ka yi ritaya don daukaka wurinka da habbaka shi.
.
A daya hannun kuma matuqar mutum zai yi wani dan wurin sana'a komai qanqantarsa ba zai yuwu a ce shi ne komai ba, misali ka yi wani dan kamfani da kake nuqa zoborodo kana zuba shi a 'yar jaka kamar shayi, ba zai yuwu a ce komai kai kake yinsa kai kadai ba, misali a ce kai ne shugaba, masinja, mai gadi, mai fita talla da sauransu, dole ka sami ma'aikata, su ma ka hana su yawon banza kenan, suna samu daga jikinka, wannan ne abinda ya dace, don aikin da ka yi a baya ya ba ka damar da za ka yi naka ne, ba wai kuma in ka gama ka dawo ka tanqwashe qafa sai dai in an yi a diba maka ba, in ka yi haka duk ilimin da ka samo ya zama na banza kenan
.
Masu bincike na qasashen Turai sun gano cewa tsabar kudi da za a saka jari duk da cewa shi ne ginshiqi na habbaka sana'a ko kasuwanci ba shi ne komai ba, kudi na da nasa gudummuwar da yake badawa na masamman amma yawaitar mutane a bangarori daban-daban na ma'aikata ko wuraren sana'a ita ce babban sanadi na habbakar wuri, misali kana da kudi kuma ka zuba su a harkokin koyarwa akwai tambayar da za a yi maka wato a wani bangare? Kana da buqatar lafiyayyen gini na zamani da aka cike shi da furanni, ka qayata dakunan karatu da ofisoshin ma'aikata, ga azuzuwa gyararru da kujeru rantsattsu, 'yan abubuwan sauqaqe rayuwa duk ka yi su.
.
A gefe guda kuma ka samo ingantattun malamai wadanda suka san abinda suke yi, ka tanadi albashin da za a riqa ba su su da sauran ma'aikatan dake wurin, ka ga ai ka gama komai, yi qoqari ka gina dakin cin abinci da dalibai za su riqa ganin ya fi musu sauqi da a ce suna dafawa da kansu, a gyara abincin da ake yi ka dan sauqaqe kudinsa, anan ma ka dawo da kudadensu aljihunka kenan, kuma ka samar wa jama'a da aikin yi, daga gefe kuma ga wani dan shagonan ka gina na kasuwanci, anan ne za a riqa kwafe wa dalibai takardunsu, ana sayar da katin waya kuma ga na'urar canjin kudi in akwai mai buqata.
.
Sannan kuma in kana da dama hatta dan shagon da za a riqa sayen qananan kayayyaki duk ka samar a cikin makarantar, qarshe dai kudin duka aljihunka zai dawo, in ka ga ba za ka iya ba, to gina dakunan wadannan abubuwan ka bayar a matsayin haya ana biyanka kudinsu, shi ma ka samar wa wasu da damar kasuwanci kai ma ka sami wata hanyar da za ka qara kudin shiga, wannan kam dabara ce duk wanda yake da idon kallo, a kowani fanni ka shiga za ka ga muna da wadannan damammakin amma natsuwa da kai hankali nesa shi yake damummu, ba ma iya tantance abubuwan da muke buqata, da wadanda rayukammu suke so, akwai hanyoyin cin nasara da dama ba ma kallonsu, bai yuwuwa ka ce komai kai daya za ka yi.
.
Yi tsari mai kyau, hau kan hanya, duk wata 'yar dama da ka samu janyo wani ku tafi tare, shi zai sami nasa, kai ma za ka dada daukaka ba tare da ka yi asarar komai ba, mu dubi filin wasan qafa kowa da irin aikin da yake yi, qarewa ma an rubuta sunansa a bayan rigarsa da lambarsa dake nuna irin aikin da zai yi da iya hurumin da zai tsaya, haka tsarin mutum a cikin lamarinsa yake, duk aikin da mutane za su yi a ma'aikatanka su ma a qarshe manufar dai kenan, a tabbatar ma'aikatar na sarrafa abubuwan da ake buqata, kuma kayan na karbuwa ta wurin saye su a duk lokacin da aka yi, wannan kuwa ba tunanin mutum guda ba ne ba aikinsa ne shi kadai ba.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```