*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 30```
.
KANA SO?
Da yawammu inda muke samun matsala kenan, mutum ransa bai kwanta da abuba sabo saboda matsalar da yake hangowa amma saboda rashin samun wani, ko shawarar da wasu suke ba shi ko tilastawar uwaye sai ka ga ya dauka, a qarshe da wahala ka ga mutum ya ci nasarar abinda yake nema, ko shawara mutum zai ba ka ya dace a ce ya san abin sosai, in ba haka ba da matsala, ba yadda za a yi mutum dan boko futuk ba abinda ya sani game da addini a ce shi ne zai riqa fada muku halas da haram, da wahala ku ci nasara.
.
A addinance ma na ga wani hadisi na Musa bn Talha da ya jiwo daga babansa cewa shi da Annabi SAW sun wuce wasu mutane a kan dabinai ya tambaya cewa "Me wadannan suke yi?" Suka ce "Aure suke musu, suna hada maza da mata" ya ce "Bana jin wannan zai amfanar" sai suka gaya wa manoman, su kuwa suka dena, da aka gaya wa Annabi SAW abinda suka yi sai ya ce "In dai hakan zai amfanar su yi mana, ni fa kintatowa na yi, kar ku ce za ku kama ni da abinda na kintata, in dai na gaya muku wani abu na ce daga Allah ne to ku yi kawai, don ba zan taba yi wa Allah qarya ba, Muslim (2361)
.
Akwai abubuwan karatu a wannan hadisin, in mutum ya gaya maka abu kuma ka san bai da masaniya a kai in ka dauka ka ga dama ne, a addinance ga dai abinda Annabi SAW ya fadanan, a zamanance kuma bai dace ba ka ba da damar da za a cilla ka wani wurin, ko matsalolin da kake gani ana samu a aure ana ba wa wanda bai san abinda ke faruwa tsakanin ma'aurata ne ba damar ya tofa albarkacin bakinsa sai ka ga ya wargaza komai, qila mutuminnan yana yi mata alkhairai masu yawa, wadanda sun fi matsalolin nasa, amma saboda rigimar da ta rincabe tsakanin matar da shi in ta zo ba za ta fadi alkhairansa ba, masu ji kuma sai su zata ba wani aikhairi ne sai su ba da munanan shawarwari a qarshe a kasa cin nasarar abinda ake so a auren.
.
Na ga wata mata da aka dinga kai-komo a kotu kan alaqarta da mijin, uwayenta suka tsaya kai-da-fata sai an raba auren, saboda abinda 'yarsu ta gaya musu, alqali ya ba da biko ba a daidaita ba, a qarshe mijin ya ce ya bi, ya bi, amma ya kasa cin nasara don haka a yi mata yadda take so, ta yi wub ta ce wallahi tana son mijinta za ta koma, daga kotun ta bi mijin, ba ta koma gida ba bare su ce sai dai ta koma dakinta ita kadai, na ga wani mutum da wasu bayin Allah suka jawo shi don ya ci arziqi, da yake yana da masifaffen wayau sai ya yi qoqari ya maida kamfanin nasa, masu shi kuma suka koma yi masa aiki, sai da aka kwashe shekara 8 a cikin wannan halin, a qarshe ya qirqiro matsala ya kore su.
.
Wallahi da idona na gani ba labari aka ba ni ba bare na yi zaton gaskiya ne ko qarya, ya kwashe labari, gaskiya da qarya, ya kai wa wadanda ba su sani ba, su kuma suka ba shi shawara gwargwadon yadda suka ji ba tare da sun san haqiqanin abinda yake faruwa ba, gogan naka ya kai su qara kotu, sai ga reshe yana neman ya juya da mujiya, ba arziqi ya janye qarar nan take ya fara neman sulhu, a taqaice dai kamfanin ya balbalce, duk lokacin da za ka nemi shawara yi qoqari ka yi da wanda ya san abinda kake ciki dari bisa dari, in ba haka ba kuwa to za a yi ba uwa ba riba, in ka dauki shawararsa ka zo ba ka yi nasara ba cikin sauqi zai ce maka "Ai ban san haka ne ba, don Allah ka yi haquri" shi kam a wurinsa an gama kenan.
.
Akwai wani da ya gama sakandare ta boko sai ya yi shawarar sake wata ta Islamiyya, haka abokansa suka riqa cewa "Wannan ai demotion ne, ya za a yi mutum ya shekara 12 a sakandare?" Mutuminnan ya ce ya ji ya gani, ya nemi taimakon Allah ya duqufa, sai ga shi ya kammala, ya yi Diploma ya fara digiri, ya yi masters, masu maganar ba su kai inda ya kai ba, sai cewa suke "Ai wallahi ba mu san hakan ne ya fi ba, ai mu ma da mun bi ka mun yi tare" da ya biye tasu da shikenan ba-wan-ba-wan karatun dan kama, na yarda da shawara amma ga wanda ya san abu ciki da bai, sannan in ka san karatu bai dace da kai ba, ko sana'a ko wani aiki kar ka bi surutun jama'a bar shi kawai.
.
Ko aure ne ka ga ba ka so, ko ba a son ka haqura kawai, ba wani zancen kunya da qarairayi marasa amfani, kai ne za ka zauna da ita, samun zaman lafiya da fahimtar juna shi ne cin nasarar aure, in karatu kake so, ka ga wanda ranka ya natsu da shi riqe shi, kuma shi din ne za ka iya kar ka bi shawarwarin wani, zai fada maka ne kawai ya barka da shi ka yi ta taburzawa, in har ba ka sha'awar zama lauya ko alqali to tun farko kar ka karanta lauyanci ko alqalanci, in ba haka ba karatun ba zai yi amfani ba, sai mutum ya ce bai sha'awar koyarwa a ransa ko kadan, amma ka ga ya karanta Education.
.
.
Na ga mutum biyu wadanda suka koyi gyaran wuta da wuyarin don su sami na cin abinci, da suka so qaro karatu sai suka fada Electrical Engineering, abin ya ba ni sha'awa, ko yaranka ne za su yi karatu lura da inda suka fi mai da hankali ka ba su shawara, sai ka ga an yi nasara a karatun, na ga wani uba da yake son diyarsa ta karanta likitanci, amma ta ce ita sam ba za ta iya ba, ya damu matuqa, na ce idan ya matsa mata ba za ta yi abin kirki ba tunda tun asali ba ta so, na ga wani uba wanda kullum sai ya jibgi dansa a kan sana'arsa amma dan ya qi yi masa biyayya, shi bai son sana'ar uban, da zan iya ba da shawara da na ce uban ya bar shi ya zabi sana'ar da yake so.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```