*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA // 31*
.
DUK ABU NAKA NAKA NE
Sakaci da rashin kulawa ko rashin sani su ne manyan abubuwan dake sanyawa mu rasa damar dake hannunmu ko mu bar ta wani ya qwace mana, da farko fara gina kanka tukun, yi qoqari ka sami ginshiqi mai qarfin gaske, kar ka yarda ka yi abu a kan jahilci, in kamfanin gyaran mashin za ka gina binciki kanka tukun, shin kana da kudin da zai ba ka damar aiwatar da wannan aikin? In ba ka da shi to ya za a yi ka samu? Ilimin aikin dai yana kanka kudin aiwatarwan ne ba bu.
.
Da farko tsaya ka karanci sana'ar da za ka fara, shiga ciki a matsayinka na mai koyo, yi qoqari ka san komai nata, kayan aiki, abubuwan da ake buqata, masu kyau da jabu, kudadensu, dadewarsu, bambance-bambancen dake tsakanin kamfanoni, lokutan da suka fi dacewa da inda ya kamata a yi saboda yawan mabuqata, ya zamanto dai a matsayinka na mai koyon aiki ba abinda ba ka sani ba, albashi in ka zo daukar ma'aikata da za su yi maka bayani kan kayan aiki da sauransu ba abinda ba ka sani ba, kuma ba wanda zai yi qoqarin cutarka ko bata maka aiki.
.
Na koyar a wata makaranta ta Misho, inda na ga hedimastan ko yaushe yana zagawa azuzuwa yana ganin darussan da ake koyarwa, da lokutan da ake koyarwan, wata rana ya amshi wani aji ya koyar ko ya yi musu tambayoyi don ganin shin abinda suke buqata malaman suke ba su kokuwa? Na yi mamakin qwaqwalwar mutumin yadda ya san komai kai har da sunan daliban, ba abinda malami zai fada wanda bai sani ba, sai na tambaya, ya aka yi ya san duk wadannan abubuwan? Sai aka ce ya koyar na tsawon shekaru da dama kafin ya kai ga riqe makarantar a hannunsa, ashe asali ma ba dan qasa ba ne, amma yana tsari mai qarfin gaske, koyarwar ta taimake shi sanin komai.
.
Idan ka gama sanin komai ya za a yi wani mutum ya zo maka daga waje ya mallake ka? Ba zai yuwu ba, na ga wata makaranta da wani ya so gudanar da ita, ya tanaji komai amma bai da kudi, sai suka hada hannu da wani mai abin hannunsa, a qarshe aka fara rigimar shin wa ma yake da makarantar tukun? Wanda ya fi qarfinka sai ya dauki hannunka ya mare ka da shi, kusan abinda aka yi kenan, mutumin farko da a ce yana da kudinsa sai ya ci gaba da gudanar da lamuransa shi kadai ba zai jawo kowa ba.
.
Duk abinda za ka yi in dai kai da qarfinka za ka yi aiki wani da dukiyarsa kar ka yarda a ce komai shi zai yi, wani zai ce kar ka damu, ko nawa kake so ni zan dauki nauyi, in ka yarda da wannan to ko shakka babu ka sayi wuqar yanka kanka, sanya taka dukiyar kuma ka yi aiki da qarfinka, ba yadda zai dawo wata rana ya yi farfagandar cewa komai nasa ne don shi ya yi, kai ma ka sanya kudinka, ka yi aiki da qwaqwalwarka sannan ka ba da lokacinka daidai gwargwado, abubuwan dake faruwa a duniya yanzu yadda ka san ba lahira a gaban mutane.
.
Akwai wata makaranta da wani ya so gudanarwa, shi ya ke da wuri a hannunsa, sai ya jawo wani babban malami wanda ya yarda da shi sosai, ya danqa komai a hannunsa, sai mutumin ya yi aiki da wannan damar ya maida mai wurin yaronsa ya yi ta yi masa bauta na tsawon shekaru, sai dai ya dan gutsuro a wata ya miqa masa, ba wanda ya san abinda ake ciki, a qarshe da yake mai wurin shi ma ba nasa ne na kansa ba sai mutumin ya kori shi wai bai gamsu da irin gudummuwar da yake badawa ba, idan kana da rai ba abinda ba za ka ji ba, wadannan su ne abubuwan da ni na gani da idona Allah ne kadai ya san abubuwan dake faruwa a wasu wuraren.
.
Da a ce mutuminnan ya koyo aikin, ya fara da kansa bai janyo kowa ba, shi yake gudanar da komai ba wanda zai zo rana tsaka ya mamaye masa wuri, balle ya tuhume shi da rashin gaskiya har a qarshe ya ce zai kore shi, duk sana'ar da za ka shiga yi qoqari ka san gabanta da bayanta yadda ba wani abinda zai boyu maka, kana da cikakken 'yanci, kana da duk wata dama da za ka dauki matakin da kake so, ba tare da wani ya yi aiki da qwaqwalwarka ya cuce ka ba, in kana gaya wa kanka cewa ba za ka iya kaza ba ina tabbatar maka daga lojacin da wani ya karbe maka wannan damar sai yadda ya yi da kai.
.
Za a kai yadda ba za ka iya zartar da komai ba sai abinda ya so, shi kuma abinda ya ce ka yi ba ka da makawa, ko kafin ka farga ya yi maka babbar illa, don duk abinda zai amfane ka ba zai yarda da shi ba, duk kuma wata hanya da za ka bi wace za ta nuna maka hanyar daidai ba zai yarda ka san ta ba, taka ta qare kenan, ka bude idanunka, ma'ana duk lokacin da ka gano cewa nasararka tana kan dakinka ne to ka gina matakalanka da kanka, ka hau da kanka ka ciro, ka sani in ka tura wani ya ciro maka to shi ma fa yana so.
Mu kasance a rubutu na gaba
Rubutawa :- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegram👇
https://t.me/miftahul_ilmi
→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna 👇
https://wa.me/2347036073248