*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA // 34*
.
BAMBANCIN HANZARI DA GAGGAWA
Hanzari yana nufin ka qara saurin tafiyarka ne don ka isa zuwa ga nasara a daidai lokacin da ake buqatarka, gaggawa kuwa na nufin ka yi saurin aikata abu tun lokacin aikin bai yi ba, kenan hanzari ake buqata ga mai son cin nasara ba gaggawa ba, domin abinda ake so shi ne mutum ya iya samun abinda yake buqata da surar da yake buqata din, mun taba zuwa tambayar wani karatu na NCE sai aka ce mana akwai "regular" shekara 3, part time shekara 4 sai kuma long vacation shekara biyar, in mutum zai iya sai ya dauki ta shekara 3 don ya yi hanzari ya gama, in ba zai iya ba kuma ya dauka to ya yi gaggawa kenan.
.
Duk wata sana'a ko aiki da mutum zai kama ya tabbatar hanzari zai yi ba gaggawaba, wata mata da aka kawo mata kishiya sai ta fara nuna wa kishiyar cewa ita keda mijin, tana saka ta ayyuka daban-daban, har amaryar ta goge idanunta ta ce ita ba baiwa ba ce, daga ranar ta dena yin komai, har da wanda ya dace ta yi din ma, ta ce matsayinsu guda ne, na ce gaskiya uwargidan ma ta yi gaggawa, da ta yi haquri ta janyo yarinyar a jiki, ta nuna mata abinda ya dace, koda an gaya wa amaryar qarya da gaskiya in ba ta ga abinda ake gaya mata ba za ta sauko ta yi abinda ya dace, ba abinda mutum zai bi a hankali sai ya ga ribarsa ko meye kuwa.
.
Na ga wani mai aski yana ta fada, da yake rigimar ba tawa ba ce sai na ja bakina, wai yaron da ya zo koyon aiki ne ya tsaya sai an riqa raba kudin da ya samu kashi biyu ana biyansa, alhali ogan yana ganin yaron ne ma zai riqa biyan koya masa da ake yi, ni dai ban sa baki ba, amma na san mai koyon aiki a wasu wuraren shi ne ma yake biya ba shi ake biya ba, kamar dai yaron ya yi gaggawa, tunda ba a ce ya biya ba bai dace ya ce a biya shi ba, a qarshe dai sun rabu, ina da tabbacin cewa indai yaron zai ci gaba da haka ko ina ya je irin wannan rabuwar za a yi.
.
Wadansu sun shirya yin wani kamfani sai suja tara kudin farko a hannun daya daga cikinsu, kusan shi ake so ma ya riqa ajiye kudin, a qarshe dai wannan kudin bai fito ba, sai a albashinsa aka riqa cirewa a hankali, kuma an amshe tarin daga hannunsa, saboda bayyanar rashin gaskiya qiri-qiri, na ce ya yi gaggawa ne, da ya yi haquri akwai wasu kudi na masamman da ake bai wa duk mai tarin kudi, da ya rabauta da shi, wanda ya fi ba ni mamaki shi ne wanda ya je neman auren wata yarinya, an ba shi ita kuma an saka masa rana, sai da ya rage saura 'yan kwanaki kadan sai ta yi maganar kayan daki ya ce yana da wani qwararren kafinta.
.
Ashe gogan naka ya bi ta kan kudin ne, auren da bai dauru ba kenan, sai gashi ana ta wasan kurar boyo tsakaninsa da amaryar, gaskiya ya yi gaggawa, da ya bari ya aure ta tukun, komai nata inda soyayya nasa ne, gajin haquri ne, wata kuma maigidanta ne ya auro qawarta ba tare da saninta ba, ya ce in ta sani za ta iya dagula lamarin, a taqaice dai ba ta sani din ba sai bayan an daura, nan fa uwargidan ta tada bala'i har ya kai ga ta bar wa amaryar mijin, da dakinta da ma yaran da ta haifa, saboda kishi, na ce ta yi gaggawa, da za ta bi a hankali da ta riqe kayanta gaba daya.
.
Akan yi gwaji ne don tabbatar da ko mutum zai yi gaggawa, duk da cewa ina tababar maganar gwaji a neman aure, wasu matan sukan yi asarar miji na gari a dalilin gwaji, na tabbata ba shi ne hanya ta qwarai wurin zabin miji na gari ba, don da shi din ne da Annabi SAW ya zabar mana, amma bincike shari'a ta tabbatar, in dai namiji ne to mace ta bar shi da kininsa kawai, maqwabta abokan aiki, 'yan uwa duk za su iya taimakawa wurin bincike, kuma su din ne za su kawo abinda ya dace.
.
Wani dan abu ne ya shiga tsakaninsu ita kuma ta nemi saki a matsayinta na mace, gaulan naka ya ba ta duk da cewa namiji ne, a kullum suna tare, bayan ba aure a tsakaninsu, sai ya zamanto duk bayan 'yan kwana biyu sai ta dauko yaro ta zo gidansa wai ta kawo masa dansa ya gani, amma sai su kwashe sa'o'i biyu zuwa uku bai gama ganin yaron ba, na ce sun yi gaggawa, da sun yi haquri za su fahimci junansu, haka dai suka ci gaba har wanda tsautsayi ya fada masa ya aure ta, ba ta jima ta fice abinta ta koma inda ta fito.
.
Wasu kuma duk an yanke musu hukunci mai tsanani akan kashe wani da suke zargin cewa ya kashe musu qani, alal aqalla da sun danqa shi a hannun hukuma, a tunanina ba mutumin da zai wuce kwanakin da Allah SW ya diba masa, matuqar dai za su iya kashe shi a wannan lokacin to sun yi gaggawa, domin ko ba su tabe shi ba mutuwa zai yi, akwai abubawa da dama da muke rasawa a dalilin gaggawa irin wannan, ba laifi ba ne su yi hanzarin miqa maganar koto kafin bincike ya kai gare shi, amma kashe shi kam gaggawa ne
Mu kasance a rubutu na gaba da yardar Allah...
Rubutawa :- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su Aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar mu 07036073248