HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 32


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA // 32*
.
MUTANE KALA BIYU NE
Dangane da aiki ko sana'a mutane sun kasu zuwa gida biyu:-
a) Mai jin dadin aikinsa: Wannan kam yana son aikinsa kuma yana jin dadin ganin abinda yake yi, kullum alla-alla yake yi gari ya waye ya kama hanya, don ko kamin ya bar aikin ya dawo gida sai da ya tabbatar ya kammala aikin yau gaba daya, kuma ya shirya abinda zai taras gobe, yakan bar aikin ne cikin zaquwar dawowa ya taras da shi, wannan ya sa wani zai gama da na yau har ya dan rage na gobe ma yadda in ya zo aikin zai yi masa sauqi.
.
Irin wadannan mutanen ba su da wani tunani na rabuwa da aikin don suna jin dadinsa, koda kuwa wurin aikin nasu ne, ko nawani ne sukan yi ne a biya su, wani ma sai ka rantse da Allah wurin nasa ne saboda qaunar aikin da yake yi, na ga wani Basakkwace da ya riqe wa wani Bakano shago da amana, na yi zaton yaron wancan ne, ashe bariki ce kawai ta hada su, har dai Bakanonnan ya yi qarfi ya sayi wani shagon kusa da wannan ya maqare shi da kaya, koda ya tashi tarewa sai ya ce ya bar wa yaronnan nasa tsohon shi ya koma sabon, lamarin ya ba ni sha'awa matuqa, bai yi haka ba sai don ganin gaskiya da amanar yaron da kuma jajurcewarsa, na ga wuraren aiki da dama amma ban ga rabuwar da ta ba ni sha'awa kamar wannan ba.
.
Wanda duk yake qaunar aikinsa za ka taras kullum neman ci-gaban aikin yake yi, yana ta nemo hikima ta kowani bangare yadda zai habbaka aikin nasa, ko ya sauwaqe shi, ko ya inganta shi, ko kuma ya qawata shi ga idon jama'a, tunaninsa a kullum shi ne ci gaba, bai damu da cewa aikin nasa ne ko na ubangidansa ba, irin wannan ne sai ka ga a qarshe ubangidan nasa ya kyautata masa sanadiyyar aikinsa, na san wani da ya je koyon aiki a wurin wani abokina ko shekara cikakka bai yi ba har ya fara tunani da fadin cewa ogan nasa bai kai shi sanin kan aikin ba, wannan a ganina butulci ne da rashin sanin ya kamata, qila kuma zaman ba zai wani dade sosai ba, saboda raini ya fara shigowa tsakiya, duk inda aka fara samun irin wannan to kuwa akwai matsala.
.
b) Yana aikin ba don yana so ba: Wannan za ka taras don dole yake yi, irin bai sami wanda ya fi shi ba, ko an matsa masa ne a gida, ko kuma bai son zaman banza dole ya fara, ko shi dan na kashewa kawai yake nema bai dauke shi a matsayin sana'a ba, a irin wannan yana yi ba dole ne ya je aiki ba, a kullum yana neman dan dalili ne wanda zai maqale da shi ya qi zuwa aikin, ko in ya je din ya dawo gida ko ya wuce yawonsa, ko bai yi aikin komai ba za ka taras da shi a gajiye yake, in damina ta zo ko hadari ya gani ba zai fita aiki ba to bare a ce an dan yi yayyafi, na ga wanda ya qi zuwa aiki da aka tambaye shi dalili sai ya ce wai mai gadin abokinsa ne ya karye kuma abokin ya yi tafiya shi ne ya je ya dan zauna masa.
.
Shi abokin ya tafi aiki, koda shi ne ya karye bai da 'yan uwa ne da za su zauna masa bare kuma mai gadinsa? Abin gwanin ban mamaki, irin wadannan mutanen ba yadda za a yi su yi tunanin bunqasa aikin bare har su yi tunanin kawo ci-gabansa, za ka iya kwatanta dalibai biyu da suka je yi wa qasa hidima a wani kamfani, daya daga cikinsu ya dage yana ta aiki tuquru, a cewarsa yana qoqarin sanin madafan aiki ne, wanda tabbas haka abin yake, na biyun kuwa yana ganin shi yi wa qasa hidima yake, bai ga dalilin da zai riqa qarar da qarfinsa a kan wani qaton banza ba, yau in ya zo aiki gobe ya qi, wani lokacin ma ya ce bai da lafiya ya yi tafiyarsa sai bayan mako guda ya dawo, a qarshe kamfanin suka dauki wancan aiki yana kammala hidimarsa.
.
Shi ma dayan ya so a ce an dauke shi don kuwa ya iya aikin kamar wancan, amma ana qimanta mutum ne da abinda yake aiwatarwa, wanda bai sha'awar aiki in ka je wurin za ka gan sa da wayarsa yana lallatsawa, ko wasa da yara ko kallon talabijin, bai da wani lokaci da zai bata don ganin ci-gaban wuri, wani ma bai damu da a kore shi ba, kamar wani mai aski da na ga yana ba yaronsa kashi, wai ya bude shagon ya je yana yi wa maqwanmbcinsa mai nama aiki don a ba shi kudin da bai wuce Naira 50 ba, ubangidan nasa ya zane shi ya ce "Duk tsiyar da za ka yi wallahi ba zan kore ka ba, kuma sai ka yi aikinnan" ya kwaso ashar dinsa ya watsa, wai ashe uwarsa ta kawo shi shi kuma ya fi son inda zai yi aiki ne a biya shi wahalarsa ba wai wurin wani koyon sana'a ba, ka ga wannan da wahala ya yi wani abin azo a gani.
.
Ina ganin akwai bambanci tsakanin qwadugo da sana'a, duka aiki ne kowa kuma da hanyar cin abincinsa, amma galibi 'yan qwadugo sukan fita ne ba tare da sanin ina za su ko wani irin aiki za su yi ba, kamar leburorin da na sani, ma'aikatan gini ne, amma ba qananan ayyuka da ba su iya ba, su ne gini, fenti, ginan rami kamar masai da rijiya, sanya wuta a daki, tabbatar da masai na korawa da ruwa da sauransu, wata rana a samu da yawa wata rana a rasa gaba daya, akan sami ranar da babu ma gaba daya, irin wannan za ka taras hatta aikin akwai yanayin lokacin da aka fi samu, akwai lokacin da ba a samun komai ma, yadda mutum ya fita haka zai dawo hannu Rabbana.
.
Amma in ka koyi aiki mai wuri tabbatacce kamar fawa, qira, shago, kanikanci da sauransu kana da matabbata, in kai mai himma ne cikin dan lokaci qarami mutum zai yi nasa, sai ka ga ya zama wani abu, a qarshe sai dai shi ma ya sami yaron da zai zauna masa, in ya yi dace shi ma ya zama babba kenan, a lokacin zai ga amfanin qoqarin da ya yi, in ya sami yaro mai qwazo tabbas zai sami cikakken lokacin da zai huta, a wannan lokacin zai fara tunanin yanzu ya za a yi ya sake samun wani wurin ya zama yana wuri biyu tunda wannan ya sami mai riqe masa? Amfanin dagewa kenan a aiki.

Mu kasance a rubutu na gaba 

Rubutawa :- Baban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegram👇
https://t.me/miftahul_ilmi

→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna 👇
https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)