YAREN SOYAYYA 02


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 002//🌹💝*

*_Wallafar:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_MANUFAR WANNAN DAN LITTAFIN_*

_Manufar wannan littafin shine:-_
  • Fahimtar da ma'aurata wasu halayyar da ke tare da su, amma yawanci ba su sansu ba
  • Bayyana hanyoyin da suka kamata a bi don wanzar da zamantakewar aure, da kuma kaucewa rashin fahimtar juna
  • Ilimantar da ma'aurata da Iyayensu bambance-bambancen da ke tsakanin daidaikun mutane, don samar da fahimta ta kwarai ba maimaita abin da wani ya yi ba
   • Nuna cewa kowane Mutum akwai abin da Allah ya sanya masa shi ne abin da yake so ko ya fi so, ko kuma qi ko ya fi qi.

*_MUHIMMANCIN WANNAN RUBUTU_*
   Idan muka yi la'akari da yawan aure da aka yi a wannan zamanin, da fahimtar mutane wayen raya Sunnar Manzon Allah ﷺ a wannan bangare, da kuma samun matsaloli da ake yi a cikin wannan aure, da yawan koke daga duk bangarori; maza da mata a kan zamantakewaa, lallai hakan zai wajabta a sake duba don bada gudunmawa wajen takaita damuwa, da kawar da matsala, da bin hanyoyin da zasu sanya aure ya zama waje na sa'ida da hutu da jin dadi, nesa da abin da ake bayyana wa mutane a fina-finai, da kuma kafofin yada labarai na nuna ai shi dama aure matsala yake dauke da ita. 
  Daga cikin muhimmancin wannan talifi shi ne; bayyanawa ma'aurata masu buqatar gyara zamantakewarsu, kan cewa lallai aure na gyaruwa koh bayan an samu matsala, kuma ana iya sauyawa sama bisa kasa, daga ba daidai ba zuwa daidai, wanda hakan takene na addininmu na cewa duk bar'na tana gyaruwa.
    Abinda zai qara sanya wannan talifi ya zama mai muhimmanci shi ne, kasancewar Iyaye da kakanni sun yi nesa da 'ya`ya, ko kuma suna shakkarsu, sabida `ya`yan sun yi karatun boko, sai suke zaton sun fi Iyayensu sani, amma kuma alal haqiqa, sun jahilci yadda zaman aure yake, kuma su iyayen ba su day kar'fin gwiwa su gaya musu abin da haqiqanin aure yake buqata, ko yake dauke dashi.
  Aure sunna ce ta Manzon Allah ﷺ , wanda ba ya son aure haqiqa ya nuna rashin sonsa ga abin da Manzon Allah ﷺ yake so. Wannan dan littafi yana koqari ne don nusar da mai karatu kan cewa:- 
  • Soyayya jigo ne a cikin aure a musulunci, kuma abu ne da ya wajaba a karfafi samuwarsa da karuwarsa 
  • Ko wane dan Adam akwai irin abin da Allah Ya sanya masa so a cikin wannan duniya. Mutum a dan wannan talifi, zai fahimci shi me ya fi so, sannan kuma yaya zai gane abin da abokin zamansa ya fi so.
  • Gano cewa yawancin sabani yana faruwa ne, ba don babu soyayya ba, amma saboda an kasa gane abin da yake janyo matsalar da take kawo sabani tsakanin ma'aurata 
  • Muhimmancin wannan talifi yana da alaqa ne da bayyana hanyoyi mafiya sauki da mutum zai bi ya mallake zuciyar abokin zamansa, sannan shi kuma ya sami rayuwa mai am-fani da sa`ada.

*_MUHIMMANCIN DAWWAMAR SOYAYYA A ZAMAN TAKEWAR AURE A MUSULUNCI_*
  
   Dukkan wani aiki da mutum yake yi ya kasu ne gida uku (3) ; ko dai ya zama yana yin aiki tare da cewa yana sane kuma da ganin damarsa, ko kuwa dai ya zama yana yin aikin ne ba tare da ya sani ba kuma babu ganin damansa, ko kuma wani ya sanya shi tilas ya yi wannan aikin ko ba tare da yana so ba. Aiki da mutum zai yi da saninsa ana kiran wannan da 
  A. "Iradiyya" ma'ana mutum yana sane, kuma radin kansa yaso ya yi wannan aikin, kamar soyayya ko kiyayya ko dukan wani, ko neman ilimi da sauransu.
  B. "Dabi`iyya" wanda shi mutum yana yinsu ba tare da ya yi la'akari da hakan ba , kamar yadda idan iska ta zo, mutum zai motsa giransa, ko kuma idan ya dirgo daga wani daki kasa zai yi ba zai iya yin sama ba, ko kuma jariri da yake kama nonon babarsa ba tare da yana da wannan ilimin ba, kamar yadda mutum yake furzar da abin da ba ya so idan ya shiga bakinsa.
  C. "Kasriyya" wato wani ya sanya mutum dole ya yi wannan aiki, kamar a dura wa mutum ruwa ko giya dole ya sha saboda an fi kar'finsa, ko a yi kokarin halaka dansa ko matarsa don ya yi wani abu ko wani abu da ya yi kama da haka.

  Aiki na farko mutum na yi ne don dayan abu biyu (2); ko dai don ya janyo wa kansa maslaha, ko kuma don ya ture wani abu da zai cutar da shi. Da wannan mutum ya bambanta da sauran halittu, saboda Allah Ya ba shi hankali na gane abin da zai cutar dashi, da kuma abin da zai amfanar da shi, kuma soyayya abu ne da kan janyo wa mutum jin dadi da annashuwa, shi ya sa dan Adam yake zabansa, kuma kishiyarta `kiyayya` na janyo damuwa da kunci da rashin jin dadi, saboda haka dan Adam yake gudun kiyayya, har ya tafi yaki saboda kawar da wannan kiyayyar.
  Shi kuwa Musulmi ya ginu ne a kan tabbatar da maslaha da kuma kawar da bar'na da cuta da qunci. Saboda haka Musulunci ya yi umar'ni da a gina aure a bisa soyayya da qauna, kuma a gujewa aure a kan kiyayya da cutarwa. Amma wani lokacin idon 👁️ dan Adam kan rufe a kan abin da yake so, tare da cewa akwai barna mai girma a ciki gare shi, kuma yakan iya kin wani abu alhali kuwa akwai maslaha mai yawa a gare shi, a wannan lokacin ne ya wajaba a nemi taimakon Allah, da shawarwarin kwararru da kuma dawowa cikin hayyaci yayin yin soyayya ko kiyayya. 

  Allah Yana cewa:- 

 كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ وَهُوَ كُرْهٌ لَّكُمْ وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ

  "Mai yiwuwa ku qi wani abu alhali kuwa alheri ne a gare ku, mai yiwuwa ku so wani abin alhali kuwa sharri ne a gare ku, Allah ne masani alhali kuwa ba ku sani ba" (Baqara: 216)
  
  A bisa wannan aka ruwaito daga Manzon Allah ﷺ 

 عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبَّاس قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ” أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِنِسَائِكُمْ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ الْوَدُودُ، اَلْعَؤُدُ عَلَى زَوْجِهَا، اَلَّتِي إِذَا آذَتْ أَوْ أُوذِيَتْ، جَاءَتْ حَتَّى تَأْخُذَ بَيْدَ زَوْجِهَا، ثُمَّ يَقُولُ وَاللَّهِ لاَ أَذُوقُ حَتَّى تَرْضَى.“

  Daga Abdullahi dan Abbas (R.A) ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Shin ba na baku labarin matayenku `yan al-jannah ba? Ita ce mai qaunar mijinta kuma take yin duk abin da zai kaunace ta, mai haihuwa, mai ba da haquri ga mijinta idan sun bata, ita ce wadda idan ta cutar da wani ko aka cuce ta, sai ta riqe hannun mijinta ta ce: Wallahi yau ba ni ba barci har sai ka yi haquri". 
  A bangaren maza kuwa Manzon Allah ﷺ sai ya bayyana su ma`yan al-jannah: 
  ﻋَﻦْ اﺑْﻦِ مَسْعُودٍ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِمَنْ تُحَرَّمُ عَلَيْهِ النَّارُ، بَلَى يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَالَ: عَلَى كُلِّ هَيِّنٍ، لَيِّنٍ، قَرِيبٍ، سَهْلٍ.
  An karbo daga Abdullahi dan Mas'ud (R.A) daga Manzon Allah ﷺ ya ce: "Ba na baku labarin wanda wuta za ta haramta a gare shi ba?". (Sahabbai) suka ce: Muna so Ya Manzon Allah ﷺ sai ya ce: "Ta haramta ga dukkan wani mai sauqin (lamari) mai taushin (hali) na kusa ba murdadde ba".
  Hadisan nan guda biyu, suna tabbatar mana da wasu sifofi na bai daya da ya kamata a sifantu da su a zaman aure, domin tabbatar da manufar Musulunci a kan lamarin aure, da kuma samar da al'umma ta gari Musulma, sannan kuma a kawar da duk wata cutuwa, a kuma tabbatar da dukkan alheri.

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu muh'd_*
Post a Comment (0)