MUTUWA BA ITA CE ABAR TSORO BA

*MUTUWA BA ITA CE ABAR TSORO BA; A KAN MAI ZA A MUTU SHI NE ABIN JI!*

*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*

Cikin taimakon Allah, a yau Litinin 28 ga watan Dhu'l-Qa'adah, 1441A.H (20/07/2020) majalisin mu na Daura wanda Sheikh Khidir Ibrahim Ƙaura Zaria ke gabatar mana, mun samu baƙuncin ɗaya daga cikin maluman mu na garin Zaria Sheikh Jamilu Abdulƙadir Assudany.

Malam ya ziyarce mu domin gaisawa da malam da kuma ƴan uwa ɗalibai. Bayan gaisawa da malam da muka yi, ya yi mana nasihohi masu muhimmanci, wanda ganin muhimmancinsa ya sa nayi wannan rubutun. Nayi ƙoƙarin taƙaita nasihohin a gaɓoɓi kamar haka:

*1) Muhimmancin ilmi da nemansa:*

Malam ya ƙarfafi guiwar mu a kan neman ilmi da kuma aiki da shi. Haka kuma, ya bayyana mana irin halin da muke ciki a yanzu da neman ilmi ya yawaita, amma kuma aiki da ilmin ya ƙaranta. Malam kuma ya jawo mana hadisi Manzon Allah (S.A.W) wanda ya ke bayyana cewa a ƙarshen zamani za a ɗauke ilmi, ta hanyar ɗauke rayuwakan maluma. Don haka, malam ya mana wasiyya da mu ci ribar lokuttan mu wurin neman ilmi wurin malaman da muke da su, tun kafin Allah ya ƙarɓesu. Musamman kuma yadda hanyoyin neman ilmi ya sauwaƙa. A ƙarshe malam ya faɗi wata magana cewa: "Ilmi baya zama ilmi, sai idan an yi aiki da shi.

*2) Neman taimakon Allah akan aiki da ilmin da mutum ya ke koya:*

A wannan gaɓar malam ya ja hankalin mu ƙwarai wurin yin aiki da abin da muke karanta. Domin babu amfani ga ilmi da aka koya babu aiki da shi. Bayan kuma mutum ya yi aiki da shi, sai ya yi kira zuwa ga mutune su ma suyi aiki da shi, domin a gudu tare a tsira tsare. Malam saboda tawadu'u irin na sa yace "Ni ma da nake muku nasihar ba wai na siffantu da su bane; amma duk lokacin da ake tunatar da juna yakan sa mutum ya dage wurin siffantuwa da ayyukan mutanen kirki.

*3) Tunawa da halin da muke ciki:*

Malam ya É—auki mintuna kusan 8 yana bayani akan wannan gabar, saboda muhimmancinta.

Muna cikin wani yanayi da musibu sun yawaita, musamman musiba ta kashe-kashen rayuka. Malam yace wasu labaran da muke ji daa daga wasu ƙasashe, muka dawo muna jinsu a kudancin ƙasarmu, ga shi yanzu sun zo mana arewa ci.

A ƙarƙashin wannan gaɓar malam ya kawo wata magana a kan masu garkuwa da mutane, bayan sunyi garkuwar kuma su buƙaci a basu wasu kuɗaɗe masu yawa.

Malam ya ce shi a ta shi fahimtar, gaskiya baya ganin dacewar a ba su kuÉ—i domin su sa ki wanda suka kama. Dalilinsa kuwa shi ne: wannan kuÉ—in da ake ba su da shi ne suke amfani wurin sayan miyagun makamai da za su ci gaba da yin garkuwa da mutane.

Don haka, mutane su dai na jin tsoro, da zarar an kama wani na su an buƙaci wani abu daga garesu, sai su takura kansu ta hanyar bin ƴan uwa suna roƙonsu su tattara abin da suke da shi su bada domin a saki wanda aka kama. Malam ya ce idan kuma su ka kashe mutum, matuƙar yana da imani bai yi mutuwar asara ba. A ƙarshe malam ya cike da wata magana wacce na baiwa rubutuna ta ke: "Mutuwa ba ita ce abar tsoro ba; a kan mai za a mutu shi ne abin ji".

Saboda haka, nima wannan ita ce fahimtata tsakanina da Allah. Kuma ina mai tabbatar muku da cewa, idan har al'ummar mu za ta ɗau wannan fahimtar da izinin Allah za a kawo ƙarshen wannan garkuwa da mutane a wannan ƙasar ta mu.

Allah na ke roƙo ya yaye mana musibu da suke damun mu, ya kare mu daga sharrin duk mai nufin al'umma musulmi da sharri, ko Kasar mu. Allah kuma ya shiryatar da su idan masu shiriya ne.

Post a Comment (0)