YAREN SOYAYYA 03

*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 003//🌹💝_*

*_Wallafawa:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

   *_MANUFAR YIN AURE A MUSULUNCI_*

  Idan mun gano cewa lallai a cikin zamantakewar aure wani abu ne da yake tasiri a farkon auren, bayan nan kuma ya yi kasa, to ya kamata kuma mu kula da cewa mu Musulmi ba wannan ne kadai abin la`akari a wajenmu ba, Musulunci ya sanya mana manufofi tabbatattu wadan da zasu sanya mu mu riqe aure har zuwa lokacin da zamu bar wannan duniyar, kuma saninsu da riqo da su ya zama wani kalubale ne ga dukkan Musulmi.
  Dan Adam mai hankali yana yin abu ne da manufa, mutum marar manufa a cikin lamarinsa daidai yake da mutumin da ya fito da safe daga gidan sa amma bai san inda za shi ba, irin wannan mutumin duk inda iska ta kada shi nan zai yi. A Musulunci mutum yakan sami lada ne gwargwadon irin niyyarsa, kuma daidai da dace da ya yi na samun dacewa da manufar addinin Musulunci.
  Ana yin aure ne a Musulunce saboda dalilai da dama, kuma sanya wadannan dalilai a gaba su ne sukan zamo sitiyari na rayuwar aure, kuma su taimaka wa mutum shanye duk wata damuwa da zai iya gamuwa da ita saboda sanin muhimmancin manufar da ta sa shi ya yi auren. Daga cikin manufofin akwai:- 

  *1- Yin Biyayya Ga Umar'nin Allah (s.w.a) Da Manzons (ﷺ).*

   Allah Mai girma da buwaya Ya yi umar'ni da a yi aure kuma Manzon Allah ﷺ ya qara bayyana wannan lamari qarara. Allah Yana cewa:-

( وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ )

  Ma`ana:- (Kuma ku aurar da marasa aure mata daga cikinku) *_(Nur:32)_*

  Kuma Manzon Allah ﷺ ya ce:- 
« يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ الْبَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ ...»

  ``Ya ku taron samari! Duk wanda yake da ikon yin aure to ya yi...``
  
  Wadannan Umar'nin daga Allah (s.w.a) da Manzonsa ﷺ sun isa abin zaburarwa ga duk wani Musulmi mai koqarin biyayya ga Allah, kuma sanin cewa aure bautar Ubangiji ne, zai sauqaqa wa mutum duk wani radadi da zai ji a ciki bayan ya gamu da abin da baya so a lokacin da ya yi aure, kuma wannan zai zame masa waqar gindi na yin haquri da matsalolin aure da zai fuskanta. 

*2- Neman Lada A Cikin Aure*

   A tsarin rayuwa ta Musulmi, yakan yi dakon sanin wani abu da Allah yake so, kuma yake ba da lada a kansa don ya aikata shi. Aure na daga cikin abubuwa a Musulunci wanda ba kasafai za a iya samun abin da ya fi shi kawo lada mai gwabi kamarsa ba. Idan mutum ya sadu da matarsa, ko mace ta sadu da mijinta akwai lada mai girma a ciki,
 Manzon Allah ﷺ ya ce:-
 
  « وَفىِ بُضْعِ أَحَدُكُمْ صَدَقَةٌ »

  ``A cikin saduwar da za ku yi da (Iyalanku) akwai lada``

  Manufa idan mutum ya sadu da iyalinsa to a wannan abin da ya yi, bayan ya ji dadi, ya debe sha'awarsa, kuma Allah kuma zai ba shi lada. 
  Manzon Allah ﷺ ya ce:- 
 
« وَلَسْتَ بِنَافِقٍ نَفَقَةً تَبْتَغِي بِهَا وَجْهَ اللَّهِ إِلاَّ آجَرَكَ اللَّهُ بِهَا حَتَّى اللُّقْمَةَ تَجْعَلُهَا فِي امْرَأَتِكَ »

   ``Babu wani abu da za ka ciyar kana neman yardar Allah, sai Allah Ya ba ka lada a ciki, har lomar da za ka sanya a bakin matarka``. 

   Ma'ana idan mutum ya kawo abinci da iyalinsa suka ci, to wannan akwai lada a ciki. A dunkule yin aure da wannan manufar wani babban Abu ne a Musulunci.

*3- Kare Kai Daga Fadawa Cikin Alfasha da Mataimakanta*

  Allah (s.w.a.) Ya umarci muminai maza da mata da su rufe idanuwansu daga kallon mata wadanda ba nasu ba, wannan yana nuna haramcin kallon matar da ba muharrama ba ga mutum ko mijin da ba muharrami ba ga mace. Tabbatar da bin wannan umar'ni yana da wahala kwarai da gaske idan ba ga wanda ya zamo yana da aure ba, wannan ne ya sa Manzon Allah ﷺ ya sifanta yin aure da cewa:-
« فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ »

   ``(Yin aure) shi ne ya fi kare ido (daga kalle -kallen haram) kuma ya fi kare farji (daga fadawa cikin alfasha)``. 
   Ko da mutum ya yi azumi, ko ya nisanci inda mata suke, wannan bai kai kamar mutum ya yi aure ba wajen kare kai daga fadawa cikin alfasha, kuma Hadisin Jabir dan Abdullahi (R.A) yana qara fito da wannan lamari quru-quru.
   عَنْ جَابِرٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَأَى امْرَأَةً فَأَتَى امْرَأَتَهُ زَيْنَبَ وَهْيَ تَمْعَسُ مَنِيئَةً لَهَا فَقَضَ حَاجَتَهُ ثُمَّ خَرَجَ إِلَى أَصْحَابِهِ فَقَالَ: « إنَّ الْمَرْأَةَ تُقْبِلُ فِي صُورَةِ شَيْطَانٍ وَتُدْبِرُ فِي صُورَةِ شَيْطَانٍ، فَإِذَا أَبْصَرَ أَحَدُكُمُ امْرَأَةً فَلْيَأْتِ أَهْلَهُ فَإِنَّ ذَالِكَ يُرَدُّ مَا فِى نَفْسِهِ »

  Daga Jabir dan Abdullahi (R.A), cewa Manzon Allah ﷺ ya ga wata mata, sai ya tafi wajen Zainab matarsa a lokacin da take jeme wata fata tata, sai ya biya buqatarsa da ita, sannan ya fito wajen sahabbansa ya ce:- ``Haqiqa mace tana fuskantowa ne da surar shedan , tana kuma ba da baya da surar shedan, idan wani daga cikinku ya ga wata mace (ta ba shi sha'awa) to ya tafi wajen iyalansa domin wannan zai kare shi daga abin da ya ji a cikin zuciyarsa``.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*

Post a Comment (0)