YAREN SOYAYYA 04


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 004//🌹💝*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

*_4- Dawwamar Da Wanzuwar"Yan Adam a Bayan Qasa_*
   Allah Ya sanya dan Adam halifa a bayan wannan kasa, kuma Ya umarce shi da ya raya ita wannan qasa ya haramta masa yin duk wani abu da zai kawo barna a ban qasa, saboda yin haka zai cutar da dan Adam, duk kuwa abin da zai cutar da `Yan Adam haramun ne aikata shi. Babbar cuta ga dan Adam ita ce a rasar da shi, a kashe koh a tauye shi, kashe dan Adam guda daya kamar kashe dukkan mutane ne baki daya, haka ma raya shi. Wannan yake nuna haramcin wani abu da zai janyo raguwar `yan Adam da kuma wajibcin bin hanyar yaduwa `yan Adam. 

*_5-Daukar Nauyin Mace A Matsayinta Na Uwa Ko `Ya_*
    Mace takan zama uwa ko mata ko `ya ko `yar uwa, duk wannan kashe-kashe daukar nauyinsu wani abu ne da Musulunci ya ba shi Muhimmancin kwarai da gaske. Uwa ita ce wanda ta fi kowa, cancantar a kyautata mata a duk rayuwa, mata kuwa ladan kula da ita ya gabata a Hadisi, `ya mace kuwa idan har sun kai biyu, to Manzon Allah ya ce:-

« مَنْ عَالَ جَارِتَيْنِ حَتَّى تَبْلُغَا جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَنَا وَهُوَ.» وَضَمَّ أَصَابِعَهُ.

 ``Duk wanda ya dauki nauyin kula da `ya`ya mata guda biyu har suka girma, to zai zo ranar alkiyama ni da shi kamar haka`` Manzon Allah ya gwama tsakanin `yan yatsunsa biyu manuniya da ta tsakiya. 
   Su ma `yan uwa mata ladan kulawa da su ba qarami ba ne, har sahabbai sukan bar auren wanda zuciyarsu take so don su kula da `yan uwansu mata.

 عَنْ جَابِرٍ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ هَلَكَ أَبِي وَتَرَكَ سَبْعَ بَنَاتٍ أَوْ تِسْعَ بَنَاتٍ فَتَزَوَّجَتْ امْرَأَةً ثَيِّبَا فَقَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ تَزَوَّجْتَ يَا جَابِرُ فَقُلْتُ نَعَمْ فَقَالَ بِكْرَا أَمْ ثَيِّبًا قُلْتُ بَلْ ثَيِّبًا قَالَ فَهَلَّا جَارِيَةً تُلَاعِبُهَا وَتُلَاعِبُكَ وَتُضَاحِكُهَاوَتُضَاحِكُكَ قَالَ فَقُلْتُ لَهُ إِنَّ عَبْدَ اللَّهِ هَلَكَ وَتَرَكَ بَنَاتٍ وَإِنِّي كَرِهْتُ أَنْ أَجِيئَتُهُنَّ بِمِثْلِهِنَّ فَتَزَوَّجْتُ امْرَأَةً تَقُومُ عَلَيْهِنًَ وَتُصْلِحُهُنَّ فَقَالَ بَارَكَ اللَّهُ لَكَ أَوْ قَالَ خَيْرَا.

  An karbo daga Jabir dan Abdullahi (R.A) ya ce:- Mahaifina ya rasu ya bar `ya`ya mata bakwai ~ Ko cewa ya yi tara- sai na Auri bazawara, sai Annabi ya ce da Ni:- ``Jabir ka yi aure ne ? Sai na ce: Na'am. Sai ya ce: ``Budurwa ko bazawara?`` Sai na ce: A,a bazawara ce. Sai ya ce: ``Me yasa ba ka auri budurwa ba da za ta yi ma wasa ka yi mata wasa, ka ba ta dariya ita ma ta sa ka dariya``. Sai na ce: Haqiqa (mahaifina) Abdullahi ya rasu ya bar `yan mata, sai na ji ba na son in auro musu budurwa kamarsu, sai ya auri bazawara da za ta kula da su ta gyara al`amuransu. Sai Manzon Allah ya ce: Allah Ya sanya maka al-barka``.

*_6- Samun Kwanciyar Hankali Da Rahama_*
    Mutumin da Allah Ya azurta shi da abubuwa na duniya mace ko namiji, ba zai sami kwanciyar hankali ba idan ba shi da mata ko ba ta da miji, wannan dalili ya sa Musulunci ya kwadaitar da yin aure don samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuci. Allah ya fada a cikin littafinsa cewa:-

( ... أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ )

  ``Ya halitta muku matanku daga kanku don ku nutsu zuwa gare su, Ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninku...`` {Rum:21}.

*Kuma Manzon Allah ya ce:*
‏« ﺃَﺭْﺑَﻊٌ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺴَّﻌَﺎﺩَﺓِ : ﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤَﺔُ »

  ``Abu hudu suna daga cikin kwanciyar hankali da jin dadi; salihar mace....``. 
   Samun nutsuwa da kwanciyar hankali da soyayya wata manufa ce ta aure tabbatacciya a Musulunci wanda mutum ya kamata ya sanya a cikin manufofin yin aur.

*_7- Rabauta Da Ni'imar `Ya`ya_*
     `Ya`ya ni`ima ce babba a rayuwar dan Adam, ba ga dan Adam kadai ba, Allah Ya nuna mana ishara har ga dabbobi yadda suke himmatuwa ba himmar wasa ba wajen kare `ya`yansu da kuma nuna musu qauna, wannan ya tabbatar mana da cewa samun `ya`ya da kulawa da su wata ni'ima ce babba ba wanda yake fahimtar haka sosai sai wanda ya rasa `ya`yan. Ba kasafai akan samun mutum ya zama daidai ba a hankalce idan ya zamo Allah bai ba shi haihuwa ba, ba qaramin gibi ake samu a cikin zuciyar wanda Allah bai taba ba shi haihuwa ba. Musulunci ya sanya yin aure ne don a tabbatar da samuwar daidaito da kuma cike wannan gibi na rashin da.
  Mutumin da ya zamanto bai san mahaifinsa ba, ko ake shakkarsa, ko kuma an san shi amma ba ta han-yar aure aka same shi ba, yana rayuwa ne daidai da matacce, ko kuma ya zama matsala ga al`umma saboda gabar da zai ringa yi da saura al-umma. 

*_8- Samar Da Musulmin Gida Ta Han-yar Iyalie_*
   Musulmin gida, wata al-umma ce ta ginu daga daidaikun mutane har suka zama jama'a suka zama al-umma. Tubalan ginin wannan al-umma su ne Musulman gidaje da suka tattaru suka tada katangar wannan gini na al-ummar Musulmi. Kowane Musulmi tubali ne a cikin wannan ginin, kuma ana buqatar tubalin ya zama mai nagarta da qarko. Idan mutum ya tarbiyyantar da gidansa tarbiyya ta Musulunci sahihiya to wannan gini sai ya yi kwari ya zama nagartacce, idan kuma tarbiyyar iyali ta samu tazgaro to lallai wannan gini ba zai yi qarko ba, sai al`ummar Musulmi su nakasa. 
  Daga manufar aure a Musulunci shi nesamar da tubali ingantacce wanda za`a hada a tada ginin al`ummar Musulmi.

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*_✍️Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Post a Comment (0)