YAREN SOYAYYA 11


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 011//🌹💝*

*_WALLAFAR:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*


*MATAKI NA BIYAR:- KWATANTAWA*
   Mataki ne mai hatsarin gaske. Mataki ne na korafi, Mataki ne na saurin kosawa, Mataki ne da mutum yake kwatanta rayuwarsa da ta wasu. Allah bai halicci mutane bai daya ba, kowa da irin halinsa kuma kowa da irin yanayin da yake samun kansa, Kuma kowa akwai wani bangare nasa da ba shi da kyau ko dadi. Yayin da ma'aurata suka shiga irin wannan yanayi, sai su koma mataki na farko, ta yadda suke ganin duk wani abu mai kyau, Amma ba na su ba, sai na wasu ma'auratan daban, ganin hakan sai ya bakanta musu rai don zaton cewa su kam ba suyi sa'ar zamantakewar ba.
  Ma’aurata a yawancin lokuta suna iya kokarinsu na boye matsalolin da suke tsakaninsu saboda dalilai da yawa; wani lokaci don nuna burgewa, wani lokaci don bakanta wa Wanda suke ganin kamar ba nasu ba ne, wani lokaci Kuma don gudun abin da zai je ya dawo. Kuma ba sa jin kunyar yin karya, za ka iya Jin namiji Yana cewa: “Ni nafi karfin matata tayi min haka!”. Mace takan iya da'awar cewa: “Ai a gidana sai abin da na fada”. Da dai irin wadannan kalmomi masu nuna su sune ke rike da komai.
   Amma a gaskiyar lamari a mafi yawan lokuta ba haka al’amarin yake ba, hasali ma kishiyar hakan ne yake faruwa, mutum yakan gano haka ne yayin da sabani ya faru tsakaninsu, Kuma aka zo Mai da magana, ko Kuma aka rabu da juna, duk da cewa rashin adalci yakan shiga cikin zantuka bayan rabuwa ko yayin bacin rai. A cikin Hadisi shahararre Hadisin ‘Ummu Zar’in’, don gudun kada matan su yaudari kawunansu sai da suka dauki alkawarin cewa ko wacce gaskiya zata fada game da mijinta.
*”ﻋَﻦْ ﻋَﺎﺋِﺸَﺔَ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻗَﺎﻟَﺖْ : ﺟَﻠَﺲَ ﺇِﺣْﺪَﻯ ﻋَﺸْﺮَﺓَ ﺍﻣْﺮَﺃَﺓً ﻓَﺘَﻌَﺎﻫَﺪْﻥَ ﻭَﺗَﻌَﺎﻗَﺪْﻥَ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﻳَﻜْﺘُﻤْﻦَ ﻣِﻦْ ﺃَﺧْﺒَﺎﺭِ ﺃَﺯْﻭَﺍﺟِﻬِﻦَّ ﺷَﻴْﺌًﺎ.“*
  *_“Nana Aisha (RA) tace: wadansu mata guda goma sha daya suka zauna, sai suka daukarwa kansu alkawari suka yi yarjejeniya akan haka cewa ba zasu boye wani Abu ba na labarin mazajensu (Mai kyau ko Marar kyau).”_*
   Wannan ya sanya malamai suke cewa yawanci idan ba irin wannan alkawari aka samu ba, to labarun da suke fitowa ba lallai su zama gaskiya ba.
   A wannan mataki mace takan hango gidan wata da mijin wata, shima namiji yakan hango gidan wani da matar wani, ba don ya aure ta ba, Amma dai Yana ganin wancan yayi sa’ar mata, shi kuwa bai yi dace ba. A bisa wannan sai ya dora wa kansa ganin bangaren da yafi kyau a rayuwar wasu, haka ita ma sai ta yi ta hango bangaren da yafi haske na rayuwar wani gidan ba tare da sunyi la’akari ko sun kula da daya bangaren ba.
   Mutum zai ji maganganu na kwatantawa tana fitowa daga bakin ma’aurata a Yanayin damuwa da rashin samun irin wannan. Idan yazo yi mata magana, yakan iya cewa: “Ki duba kiga matar wane” “Kibkalli gidan wance”. Dubi yadda Mata suke ado, amma ke gaki nan ballagaza”. Da jumloli masu nuna kwatantawa da wasubko wata. Haka ita ma takan fada: “Tab! kunyi sa’a ni mijina ai sam!”, “Wance ta yi sa’ar miji, mutum mai saukin Kai, Amma ni!!!”.
  A wani salo na yaudarar zuciya, idan mutum yaji irin wadansu zantukan na wani gidan, sai yayi ta farin ciki, Kuma Yana takaicin cewa shi bai sami irin wannan ba. Wannan mataki shine yake daidai da kishiyar matakin Farko, a matakin maganadisu. Kyawawan abubuwan mutum yake kallo ya rufe idonsa wajen ganin maras sa kyau, Amma a wannan matakin sai ya juya lamarin, munanan abubuwan kawai yake duba, ya rufe idonsa daga ganin masu kyawun. Shi yasa suke fadi a waken larabci wanda ake nasabtawa ga Imam Shafi’i cewa:
وعين الرضا عن كل عيب كليلة *** ولكن عين السخط تبدي المساويا
  (Duba da) idon yarda mai kanne dukkan wani laifi ne *** Kamar yadda (kallo da) idon bacin rai mai bayyana dukkan munanan abubuwa ne.
   A matakin Farko, tana kallonsa ne da idon yarda da idon kauna, saboda haka komai idan yayi sai ta fassara shi da ma’anar soyayya. Amma lokacin da rai ya baci, aka zo wannan mataki dukkan abin da zai aikata, to wannan abin aibi ne saboda idon da yake kallon wannan abu cike yake da gaba. idan wani ya kalle ta, ko yayi Mata magana, sai ta ga yayi fushi, sai ta fassara wannan da cewa tsananin kaunarta ne, amma a wannan mataki da wani zai yi mata magana ko ya kalleta, sai ya nuna bacin ransa sai ta fassara yin hakan da yayi da cewa; Yana tuhumarta ne, ko Yana zarginta, ko ya cika zafin kishi ba gaira ba dalili.
  Idan ba ayi hattara ba a wannan kwatanta Kai da wasu a lamarin aure, idan ba a yaba da kokarin juna ba a wannan mataki, idan ba a kalli bangarorin nagarta da kyau na abokin zama ba a wannan mataki, sai tunanin da aka gina shi akan zato da wata rayuwa ta almara tayi rinjaye acikin zuciya. Kuma mutum ya hadu da ciwon zuciya na kunci da ganin kamar shi ya rasa komai na Jin dadi lamarin aure. Idan har ba a magance hakan da wuri ba, ta hanyar mutum ya zauna yayi tunanin da ya kamata, sai ya yanke shawarar ficewa daga dajiyar aure, ta hanyar sulalewa ko yanke igiyar, wannan shine mataki na karshe.
            *_LABARI:_*
   Wata Rana wani miji da matarsa sai suka tafi gidan ajiye dabbabobi (Zoo) sai suka tarar da wani biri da biranya suna ta wasa suna nishadi da juna, abin gwanin ban sha’awa.
  Sai matar wannan Mutumin tace “Subhanallah! Dubi irin wannan soyayya da take tsakanin su” (*Kwatantawa) Mijin bai ce komai ba, sai suka yo shawagi suka zo inda zakuna suke, sai yaga taking zaune can gefe ya dake yayi shiru, ita ma matar acan gefe guda.
  Sai wannan matar ta sake cewa; “Subhanallahi! Dubi irin wannan nisantar juna, ba ko kauna da soyayya a tsakanin su” (*Kwatantawa)
  Nan ma mijin bai ce komai ba, sai ya dubi wata kwalba ta lemo da yake hannunsa ya gama sha, ya cewa matarsa: “Jefa wannan kwalbar cikin kejin da zakin nan yake ciki mu gani, ki nufi samun matarsa da ita”. Z
(*Hakikar lamari)
Sai ta dauka ta jefa, take sai ga Zaki yayi wata irin zabura yayi gurnani don yaje ya Kare matarsa. sai suka koma kejin biran nan. Yace da ita ta jefa kwalban lemonta kan matar birin nan. Tana jefawa sai birin nan ya ruga a guje ya haye bishiya ya bar matarsa don gudun kada kwalbar ta fado masa.
Sai mijin Yace da ita: “Kada ki yaudaru da abin da mutane suke bayyana miki a gaban ki” Birai sun fi zakuna yawa saboda haka sai anyi hattara. Yayin da mutum yake yaro, idan mahaifinsa ya hana shi wani abu, ko ya tilasta shi yin wani abu, sai ya fahimci wannan a lokacin kamar tsana, ko rashin kauna, Amma idan girma yazo masa, sai yayi wa mahaifinsa godiya da addu’a, saboda abin da yayi masa lokacin da yake karami, Kuma wasu suyi da-na-sanin da kaico cewa ba su sami irin wancan takurawar da aka yi wa wasu ba.
*TAKAITACCIYAR SIFFAR WANNAN MATAKI:*
●Rashin ganin kyawun duk abin da abokin zama yake da shi.
● Kwatanta rayuwar da rayuwar wasu ma'auratan ko masoyan.
● Kallon bangaren aibuka ba bangaren kyau da nagarta ba.
● Sanya wa rai damuwa da neman yin shiga rayuwar almara da mafarki.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Post a Comment (0)