Fassara Waƙar Kabhi kabhie Mere Dil Mein - Part I
• Waƙa - Kabhi kabhie Mere Dil Mein - Part I
• Fim - Kabhi Kabhie
• Shekarar Fita - 1976
• Harshe - Hindi = Hausa
• Sauti - Khayyam
• Rubutawa - Sahir Ludhianvi
• Kamfani - EMI
• Rerawa - Mukesh
• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman
• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai
Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.

• Ke jaise tujhko banaya gaya hai mere liye
Cewa lallai an halicce ki ne kawai saboda ni.

• Tu ab se pehle sitaron mein bas rahi thi kahin
Kafin yanzu kina rayuwa ne a tsakanin taurari.

• Tujhe zameen pe bulaya gaya hai mere liye
An kira ki zuwa duniya ne kawai saboda ni.
• Tujhe zameen pe bulaya gaya hai mere liye
An kira ki zuwa duniya ne kawai saboda ni.
• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai
Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.
• Ke yeh badan yeh nigahein meri amanat hai
Cewa wannan jikin da waɗannan idanuwan duka nawa ne.

• Yeh kesuon ki ghani chhaon hai meri khatir
Inuwar goran kitsonnan duk nawa ne.
• Yeh honth aur yeh baahein meri amanat hai
Waɗannan laɓɓan da waɗannan hannayen nawa ne.
• Yeh honth aur yeh baahein meri amanat hai
Waɗannan laɓɓan da waɗannan hannayen nawa ne.
• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai
Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.
• Ke jaise bajhti hai shehnaiyan si raahon mein
Cewa bushe-bushen (shagullan) aure suna tashi akan hanya.

• Suhaag raat hai ghoonghat utha raha hoon main
Kamar daren tarewarmu kuma ina yaye miki mayafi.

• Simat rahi hai tu sharma ke apni baahon mein
Kuma kina tahowa ga hannuwana cike da kunya.
• Simat rahi hai tu sharma ke apni baahon mein
Kuma kina tahowa ga hannuwana cike da kunya.
• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai
Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.
• Ke jaise tu mujhe chahegi umar bhar yoon hi
Cewa za ki so ni har abada kamar haka.
• Uthegi meri taraf pyar ki nazar yoon hi
Cewa za ki kalle ni cike da so kamar haka.
• Main jaanta hoon ke tu gair hai magar yoon hi
Na san cewa ke baƙuwa ce a wajena, amma duk da haka.
• Main jaanta hoon ke tu gair hai magar yoon hi
Na san cewa ke baƙuwa ce a wajena, amma duk da haka.
• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai
Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.
• Kabhi kabhie mere dil mein khayal aata hai
Wasu lokutan, nakan ji wani irin abu na fitowa daga zuciyata.
©️✍🏻
Jamilu Abdulrahaman
(Mr. Writer)
Haimanraees@gmail.com