Buri Uku A Duniya
Sarƙaƙiya guda uku
Tai sansani a zuciya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya.
Sarƙaƙiya guda uku
Tai sansani a zuciya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya.
Daure masoyi daure daure
Ka san lago na zuciya
Ka san abin buƙatar ruhi
Sarƙa ta sarƙe zuciya
Ni na yi durƙuson
Gwiwoyi kuka ka bi idaniya
Tanyo nake buƙata gunka
Buri uku a duniya
Na zo da mazubin ƙoƙona
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya.
Ma-dama rayuwa na nan
Ruhi fa za ya wazaya
Ma-dama zuciya na nan
Buri fa za ya antaya
Ga rai da lafiya na nan
Tilas jiki ya hau ƙaya
Tsumma maƙunshe cuta na nan
Sarƙaƙiya ƙarangiya
Buri fa yai wa ruhi zobe
Sarƙa ta ɗaure zuciya
Buri uku a duniya
Buri uku a duniya.
Buri uku a duniya
Sun zam mini ƙarangiya
Sautin bugu na zuciya
Ya sa jiki galauniya
Sarƙaƙiya ƙarangiya
Buri uku a duniya
Burin cikinta zuciya
Na kasa buɗe zuciya
Ɗa zai ɓace a ragaya
Ceto jiki da zuciya.
Ruhi duka da zuciya
Fansa gareki gimbiya
Na gamsu babu karaya
Zan baki duka zuciya
Komai da ke a duniya
Nau'in dukkansu dukiya
Tarin kuɗi da dukiya
Garken awaki saniya
Fansa gareki gimbiya
Burinki dukka duniya