WAƘAR AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA
Tarnaki
Tarnaƙi hana miƙa 3x
Majaujawa sai cillawa
Sasari kuma ɗaurewa
Tarnaƙi mai zargewa
Takunkumi mai shaƙewa
Tarko mai kamawa
Turaku ko na ɗaurewa
Sarƙa rikicin gangan ƙasar uwa da uba nawa
Tarnaƙi hana miƙewa
Sasari hana rugawa
Garƙami wandon ƙarfe masaka ba ya zaunawa.
Tarnaƙi hana miƙewa
Sasari hana rugawa
Garƙami wandon ƙarfe a saka ba a zauna ba.
Ubangiji masanin gaibu da baɗini da faken kowa
Adalin sarki rabbu da yai hanin cutar kowa
Mai huwacewar mulki daidai da halayyar kowa
Na taho da buƙatata tsare ni kadda amin arwa, tsare ni kadda a min arwa.
Ɗan Aminatu tsanina da so da koyin halaye
Mai gidan asahabati da ahal baiti da sufaye
Mai ɗabi'u kyawawa gami da tsarkin halaye
Nai riƙo da abin ƙauna abin yabon sarari har ɓoye, sarari har ɓoye.
Kama zuwa daga 'yancin kai zuwa a yau ban kore ba
Ina batun ilimi namu hallanzu dai ba mu ƙosa ba
Da tattalin arzurƙanmu zuwa a yau ba mu kama ba
Bare a kai ga ginin birane har yanzu ba mu wuce ƙauye ba
A shekara hamsin baya magani ba mu samar ba
A shekaru hamsin har yau ko Keke Napep ba mui ba
Industry ba ta zauna ba
Ruwa na sha ba mu samar ba
Da laturun ba ta zauna ba
Ga agric ba mu kama ba
Ga ilimi ba a samu ba
Rayuwa ta ƙabilanci, rikicin addinanci ba inda ba mu yi asasi ba.
Ƙasar da ba ta da jirgin kanta ɗiyanta na zazzagawa
Ƙasar da ba ta asusun kanta ɗiyanta ke da kuɗin cashewa
Ƙasar da babu zani a jikinta ɗiyanta ke da zanin ɗaurawa
Mutum guda a cikin 'ya'yanta dubu ɗari da ta haifawa
Ya tattare arzurƙanta yana rawa da bazar kowa
Suna kiɗa da bazar kowa
Wai ma'aikata aka samarwa ko 'yan yasa muka samarwa?
Wai 'yan ceto muka zaɓowa ko cuta muka ɗaukowa?
Wai ɗalibai muka yayewa ko ɓeraye muka yayewa?
Ƙasar babata, ƙasar abbana, Nijeriya ta.