YADDA ZA KA CI GALABA AKAN SHAIƊAN


YADDA ZA KACI GALABA AKAN SHAIƊAN
-
GABATARWA:
Muhammad Umar Baballe 
-
"Shaiɗan la'ananne wata halitta ce da malamai ma kansu suka ƙarawa junansu ilmi wajen fayyace cewa shin shima acikin jinsin mala'iku yake, ko kuwa acikin jinsin aljanu yake, to wannan dai ba shine abinda dubawa ba, abinda dubawar anan shine sanin hanyar da za kabi domin ka kuɓuta daga kaidinsa ƙullalle"
-
"Shaiɗan ya sha alwashi a gaban Allah, a daidai lokacin da Allah maɗaukakin sarki ya fifita annabi Adam akansa, ya kuma umurce shi dayin sujjada ga annabi Adam alaihissalam, sai shaiɗan yaƙi yayi, sai Allah ya kore shi daga cikin rahamarsa"
-
"Daga nan ne sai shaiɗan ya ɗauki alwashin sai ya dilmiyar da dukkanin ilahirin zurri'ar annabi Adamu domin goge wancan takaici na nesanta shi daga rahamar Allah da akayi"
-
Dalilin haka sai ya zamto cewa kowa yana cikin hatsarin shaiɗan sai wanda Allah ya tseratar, to kaima domin neman tserata daga gareshi kanada aiyuka a gabanka, amma ga kaɗan daga cikinsu:
-
💦Yawan ambaton Allah.
💦Neman kariya daga shaiɗan.
💦Zikiran safiya da maraice.
💦Nisantar aiyukan shaiɗan.
💦Nisantar abinda Allah ya hana.
💦Zaƙewa aiyukan ɗa'a ga Allah.
-
"Waɗannan hanyoyi ne kaɗan daga cikin waɗanda za kayi ta'ammuli dasu wajen yin katanga a tsakanin ka da shaiɗan, musamman ma juriya wajen aikata kyawawan aiyukan da zasu daɗa kusantar dakai izuwa ga Allah"
-
"Wannan wani faɗa ne da yake a tsakãninka da shaiɗan, wanda kuma dole sai ɗaya yayi nasara akan ɗaya, kodai kayi nasara akansa, ko kuma shi yayi nasara akanka, amma idan ka nemi taimakon Allah sai kaga kaine kayi nasara akansa"
-
Ya Allah ka bamu ikon yin nasara akan shaiɗan la'ananne, Ameen.
-
✍🏿
Muhammad Umar Baballe
Post a Comment (0)