NEMAN RA'AYIN BAZAWARA KAFIN A AURAR DA ITA


*NEMAN RA'AYIN BAZAWARA KAFIN A AURAR DA ITA.*
.

Sheikh Solih bin Fauzan Al-Fauzan ya faďi a cikin littafinsa na
تنبيهات على أحكام تختص بالمؤمنات:

Bazawara kuwa ba a aurar da ita sai da izininta, kuma izininta shi ne ta fada da bakinta, sa6anin budurwa da aka sanya shirunta ya zama izininta. Ibnu Kudamah ya ce a cikin Al-Mugni (6/493):

Ba mu san wani sabani ba tsakanin malamai cewa izinin bazawara shi ne magana da bakinta, saboda hadisin da ya zo; kuma saboda harshe shi ne mai fadar abin da ke cikin zuciya, kuma da shi ake lura a ko ina aka ce a nemi izini.
.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya, Allah Ya ji kansa, ya ce a cikin Majmu'ul Fatawa (32/39-40):

Mace bai kamata wani ya aurar da ita ba ba tare da izininta ba, kamar yadda Annabi (ﷺ) ya yi umarni. Idan ta qi, to ba za a tilasta ta ta yi aure ba, sai dai yarinya karama (da ba ta kai munzalin balaga ba); ita ubanta yana da damar ya aurar da ita. Ita babu izini a gare ta. Amma bazawara wadda ta balaga, be halatta a aurar da ita ba tare da izininta ba; bai halatta ba ga uba, ko ga waninsa. Wannan kuwa ijma'in musulmi ne. Hakanan budurwa da ta balaga bai halatta ga wani in ba uba ko kaka ba, ya aurar da ita ba da izininta ba. Shi ma wannan ijma'in musulmi ne. Amma uba da kaka, su ya kamata gare su su nemi izininta. Kuma malamai sun yi sabani shin neman izinin nata gare su wajibi ne, ko Mustahabbi ne? Ingantacciyar magana ita ce cewa wajibi ne. Kuma wajibi ne ga waliyin mace ya ji tsoron Allah wajen wanda zai aurar da ita gare shi. Kuma lallai ya duba mijin shin ya dace da matsayinta ko bai dace ba; domin an sa shi ne ya aurar da ita don maslaharta, ba don maslahar kansa ba.
.

Wannan shi ne matsayar shari'a game da aurar da mace bazawara. Allah Ya sa mu dace.
.

*📚Irshadul Ummah.*
WhatsApp: 08166650256.
Post a Comment (0)