SHARHIN FIM ƊIN NEW YORK


SHARHIN FINA - FINAI
                       FITA TA (6) 2021

Shiri ne da yake zuwa duk ranar Litinin wanda ake zaƙulo fina - finan India ɗaya bayan ɗaya ana sharhi ko tattaunawa akai, a wannan zaure ƙarƙashin jagorancin


A wannan makon muna tafe ne da sharhin fim ɗin "NEW YORK" na jarumi John Abraham.

                    GABATARWA 

"NEW York" fim ne na India da aka fitar a shekarar 2009. Kabir Khan ne ya bayar da umarni, Aditya Chopra ya shirya ƙarƙashin kamfanin su na Yash Raj Films (YRF), tsarawa kuma Sandeep Shrivastava. John Abraham, Katrina Kaif, Neil Nitin Mukesh, Irfan Khan da Nawazuddin Sidsiqui ne suka jagoranta.
     An fara New York ne daga shekarar 1999 zuwa 2008, yana bayar da labarin wasu ɗalibai 3 da suke karatu a ƙirƙirarriyar jami'ar jaha dake garin New York ta ƙasar Amurka wanda rayuwarsu ta sauya daga harin 11 ga watan satumba da abubuwan da suka biyo baya.

                    LABARIN FIM ƊIN 

An fara fim ɗin ne da nuno inda hukumar FBI ta cafke Omar Aijaz matashin musulmi ɗan asalin Delhi a Amurka, bayan samun bindigogi da akayi a taksi ɗinsa. Sai aka tsare Omar ake tuhumarsa wanda jami'in hukumar ne Roshan ke gudanar da hakan wanda shima musulmi ne daga yankin kudancin Asia wanda ke zaune a ƙasar ta Amurka tsawon shekaru 20. Omar ya gano cewa FBI ne suka shirya masa haka domin su tirsasa shi kan yayi yayi musu leƙen asiri wajen tsohon abokin karatunsa, Sameer "Sam" Sheikh, wanda yayi shekaru 7 be ganshi ba, kuma FBI sunyi yaƙinin cewa ɗan ta'adda ne. Ana haka, Omar ya gano cewa Sam ya auri Maya wacce shi Omar ɗin yake so a lokacin suna jami'a sannan ya gano cewa har sun haifi yaro ɗaya mai suna Danyal.
     Roshan ya umarci Omar daya faɗa masa duk abinda ya sani game da Sam. Daga nan sai akayi flashback (abubuwan da suka faru a baya) wato abubuwan da suka faru tun daga watan Satumba 1999, a lokacin da Omar ya fara karatunsa a jami'ar jaha ta New York, ƙulla ƙawancensa da Maya wacce ya fahimci cewa duk da kasancewar an haife ta a New York kuma anan ta girma ta ƙware sosai a yaren Hindi, saboda ra'ayin mahaifiyarta ga fina - finan bollywood zuwa 
 haɗuwar su da Sam ba'amurken musulmi wanda shima ƙwararre ne a yaren na Hindi saboda kasancewar mahaifinsa farfesa ne akan nazarin yaren. Da ƙulluwar abokantakar su gaba ɗaya har basa son rabuwa da juna cikin shekaru biyu, da fara son Maya da Omar yayi daga baya ya fahimci tana son Sam har zuwa inda ya nisance su, ana haka kuma sai harin Satumba ya abku.
     Sai aka dawo kan labarin inda Omar ya amince zai taimaki Roshan idan har hakan ne zai tabbatar da cewa daga shi har Sam ɗin babu hannunsu a ciki (ba masu laifi bane). Sai ya koma wajen Maya da Sam yana zaune a wajensu duk wannan yana leƙen asiri ne wa FBI. Omar ya fahimci Maya 'yar gwagwarmaya ce wajen kare haƙƙin ɗan Adam wacce take taimakawa ɗaya daga cikin ma'aikatan Sam mai suna Zilgai dan shawo kan matsalar da yake fuskanta matsayinsa tsohon wanda aka tsare dangane da harin Satumba. Wanda daga ƙarshe aka sake shi sakamakon rashin ƙwaƙƙwarar hujja.
     A zaman da Omar yayi ya gano cewa bayan kwana 10 da abkuwar harin an kama Sam kuma har tsare shi har na tsawon wata 9 a matsayin zargin da ake masa na ta'addanci, case ɗin da kowa ciki harda FBI da kuma Roshan suka yarda da cewa ba hakan bane. Bayan an saki Sam saboda rashin rashin shaida amma tasirin tsarewar da akayi masa da kuma azabtar dashi da akayi ta canza Sam gaba ɗaya hakan ya saka masa tsananin tsanar FBI. Nan Omar ya gano cewa Sam yana shirya ta'addanci domin ɗaukar fansa.
     A ƙoƙarin da Maya take wajen fitar da Zilgai har wani jami'i ke ƙoƙarin yi mata rashin daraja, shine sai ya harzuƙa ya mayar da ita gida daga ƙarshe ya sheƙe jami'in a wannan daren shima hakan ta kai shi da sheƙe kansa bayan artabun tsere da suka sha shi da jami'an tsaro.
     Maya, Omar da Roshan sunyi ta ƙoƙarin hana Sam aikata abinda yayi niya na ta'addanci ta hanyar faɗa masa cewa idan har ya aikata mutane da yawa zasu wahala kamar yadda yake shima. Daga ƙarshe dai ya gamsu a inda ya miƙa wuya kuma ya fasa tashin nakiya a ginin hukumar FBI. Duk da haka a lokacin da ya ajiye wayar hannunsa (wacce ita ce asalin wadda yaso amfani da ita wajen tashin nakiyar) sai kawai aka sami wani gwanin harbi ya harbo shi har lahira, haka wayar ta faɗi ƙasa ba tare da komai ya faru ba. Nan Maya ta ruga gare shi ita ma aka harbe ta Omar kuma ya zube anan saboda kaɗuwa.
     Omar ya ƙire Danyal a matsayin ɗa, Roshan kuma ya sami yabo game da taimakawa wajen yaƙar ta'addanci. (abin dai sai wanda ya gani).

                         SHARHI 

Fim ɗin New York fim ne da ya nuna halin da musulmi da kuma baƙin haure suka shiga a ƙasar Amurka na zargin ta'addanci bayan faruwar harin watan Satumba (September). Fim ne daya sami yabo sosai daga critics daban daban daga faɗin duniya, musamman ma irin ƙoƙarin da Katrina Kaif da kuma Neil Nitin Mukesh suka yi wanda ya janyo musu samun nomination na Filmfare Awards for the best actor and best actress. A ɓangaren kasuwanci kuma ya kai matakin Super Hit a Box Office India.

                  TAURARIN CIKI 

John Abraham - Sameer "Sam" Sheikh
Neil Nitin Mukesh - Omar Aijaz
Katrina Kaif - Maya
Irfan Khan - agent Roshan
Nawazuddin Sidsiqui - Zilgai

                  WAƘOƘIN CIKI

1. Hai Junoon
2. Mere Sang
3. Tune Jo Na Kaha
4. Aye Saaye Mere
5. Hai Junoon (remix)
6. Mere Sang (remix)
7. Sam's theme
8. New York theme

          Masha Allah duka duka anan muka kawo ƙarshen wannan shareni na wannan ƙayataccen shiri mai suna "NEW YORK" sai kuma Allah ya nufe mu da ganin mako mai zuwa dan kawo wani sabon shirin. Fatan dai ana samun nishaɗantuwa da wannan ɗan shirin namu. 🙏
Post a Comment (0)