AIKI BA KAMA HANNUN YARO


AIKI BA KAMA HANNUN YARO 

Allah Ya ce: “Shi ne wanda Ya samar da ku a bayan kasa, kuma Ya umarce ku da ku raya ta”. Hud:61

Musulmi takensa; aiki ba kama hannun yaro a wannan duniya, aikin lahira da na duniya, a wajensa duk ibada ne
 
Kyautata sana’a, neman na halal, dogaro da kai, taimakon marasa shi da rauni, rashin gurbata wannan duniya, duk aikinsa ne
 
Daga Anas dan Maliki ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: “Idan an busa alkiyama, ya zamanto a hannun dayanku akwai iri na dabino da yake son shukawa, to idan har zai iya shukawa kafin ta tashi, ya shuka”. Imam Ahmad/ Ibnu Majah/ Bukhari a “Adabul Mufrad”. 

Shekaru nawa dabino yake dauka kafin ya fito, ya yi ‘ya’ya har a amfana? 

Kai yaya ka fahimci aiki da neman halaliyarka? saboda kanka ko iyalanka ko ‘ya’yanka
 
Ibada ko wahala? Sai don dole ko kuwa kana da sha’awa? 

Sallolinka da karatukanka na addini na hana ka yin sana’a don kana ganin bata lokaci ne ko kuwa? 

Watakila lokacin aiki na cinye maka yin ibada saboda haka ka tsani aiki saboda ba ibada ba ne?


Daga
Miftahul ilmi

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)