HUKUNCIN SANYA TOZALI GA MAI AZUMI


HUKUNCIN SANYA TOZALI GA MAI AZUMI 

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

*TAMBAYA*❓


Slm alkum, malam ina fama da ciwon idone, kuma sai akabaini wani kwalli inrika sawa. Shin ya hallarta insa alhali ina Azumi? Allah ya saka da mafificin alkhare.


*AMSA*👇

Wa alaikumus salam.
Dangane da wannan Mas'alar akwai ra'ayoyi kala biyu daga Malamai kamar haka :
1. Akwai Malaman da suke ganin halaccin sanya tozali ko kuma wani magani a idon mutum yayin da yake azumi. Koda dandanon abun ya kai ga Makogoronsa ko bai kai ba.
Sun dogara ne da cewa ai idanu ba wajen shigar da abu bane zuwa cikin cikin Dan Adam. Sannan ga hadisin Sayyiduna Anas bn Malik (ra) cewa "SHI YA KASANCE YAKAN SANYA TOZALI ALHALI YANA AZUMI".
Malaman da suka tafi akan wannan fahimtar sune Mazhabin Shafi'iyyah da Hanbaliyyah ka'dai. Sai dai kuma Ibnul Mundhir ya ruwaito irin wannan fatawar daga Imamul Auza'iy da Ibraheemun Nakha'iy da Hasanul Basariy Basariy da Abuth Thawr (Allah ya rahamshesu).
Daga cikin Sahabbai kuma an ruwaito irin wannan fahimtar daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar da Anas bn Malik da Ibnu Abee Aufa (Allah shi yarda dasu).
Imam Malik a Mazhabinsa bai halatta mai Azumi ya sanya tozali ko magani a idanunsa da rana ba. Idan kuma ya sanya tozalin ko maganin kuma dandanonsa yaje ga Makogoronsa, to azuminsa ya karye. Zai rama guda daya.
Sai dai ya halatta ka sanya tun cikin dare ko kuma lokacin suhur. Kuma koda kaji dandanonsa da rana acikin Makogoronka to wannan babu komai.
Imamu Malik ba ya aiki da waccan fahimtar domin babu abinda ya inganta daga Annabi (saww) acikin wannan Mas'alar. Haka shima Imamut Tirmidhiy ya fa'da.
Kabi wannan fahimtar ta Imamu Malik domin fitar da kanka daga Kokonto.
Sai dai idan idanun naka ya tsananta ciwon yadda dole sai an rika sanya magani akai akai, to sai ka koma bisa wancan Fatawar ta farko.
WALLAHU A'ALAM.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)