KWANAKIN DA AKA HARAMTA YIN AZUMI A CIKIN SU

*KWANAKIN DA’AKA HARAMTA YIN AZUMI CIKINSU* 

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum.
Malam Ina yini.
Wata tambayar kuma.
Ko akwai ranar da akayi haramcin yin azumin nafila a cikin ta.


*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

1.Ranakun Idi guda biyu, Idi babba da Idi Krama, saboda Fadin Umar dan khattab Allah yakara masa yarda:(“Lallai wadannan kwanaki guda biyu manzan AllahSallallahu Alaihi Wasallam: yahana Azumi a cikinsu, Ranar da kuke shan daga Azuminku, da ranar da kuke ci daga yankanku”Muslim).

2.Kwanaki uku na shanyan nama(Ayyamut-ta
shreeq) wato kwanakin babban sallah guda uku, Sha daya da sha biyu da sha uku ga watan zulhijjah, Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam: ya aiki Abdullahi dan Huzafah Allah yakara masa yarda yana kewayawa a muna yana cewa:(“kada kuyi Azumin wadannan kwanakin, domin su ranaku ne na cin da sha da ambaton Allah madaukakinsarki” Ahmad). Amma wannan banda mahajjaci, meyin tamattu’i da meyin Qiraani idan beda Hadaya.

3.Ranakun da mace take Haila da Bik’i, Saboda fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: a gameda hakkin mace, yace:(“Ba idan tayi haila bata sallah ba? To wannan shine tawaya-rashin cikan- addininta”Bukhari). Kuma malamai sunyi Ijma’i wato basuyi sabani ba akan bacin Azumin me haila da me bik’i.

4.Azumin mace idan mijinta na gari se idan ta nemi Izininsa,Saboda Fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam: (« Kada mace tayi Azumi alhali mijinta yana nan sedai idan da Izininsa amma banda Azumin ramadan »Bukhari da muslim).

 *RANAKUN DA AKA KYAMACI YIN AZUMI CIKINSU(KARHANCI)* 

1.Yin Azumin Ranar Arafa ga mahajjaci wanda yake tsayuwan Arafa, Saboda Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam:(“ Ranar Arafada Ranar yankawato layya-, da kwanakin Shanya nama wato kwanakin idi uku-Idinmu ne mu musulmai, kuma su kwanakin ci ne da sha”Abu dawud Tirmidhi).

2.Yin Azumin Ranar juma’a ita kadai, Saboda Fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam:(“ kada kuyi Azumin ranar juma’ah ita kadai,sedai kafinta da rana daya ko bayanta da rana daya”Bukhari da muslim)

3.Yin Azumin Ranar Asabar ita kadai, Saboda Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam:( “kada kuyi Azumi ranar Asabar, se wanda aka wajabta maku ,idan da É—aya daga cikinku besami komaiba se bawon Inabiko itacen bishiya to ya tattaunashi”Ahmad da Abu Dawud).

4.Azumin Shekara: Shine mutum yayi Azumin Shekara gabadaya ba tare da shan ruwa ba , Saboda Fadin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam:(“Babu Azumi ga wanda yayi Azumin shekara”Bukhari da muslim). da Fadansa:

5.Zarcewa da Azumi kwana biyu a jerekofiye da haka da gangan batare da ya sha ruwa ba, shine abinda ake kira da wisaali, Saboda Fadin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam:(“Ina kashedin kudayin wisali”Bukhari da muslim). Da fadansa:(“Kada ku zarce wato dayin Azumi-duk wanda yakeso yazarce, cikinku to ya zarce zuwa lokacin Sahur”Bukhari).

6.Azumin Ranar shakka, itace ranar talatin ga watan sha’aban saboda Fadin Ammar bin Yasir Allah yakara masa yarda:(“Dukwanda yayi Azumin ranar da ake shakka to hakika ya sabama Abul-qasim, Sallallahu Alaihi Wasallam”Abu Dawud da Tirmidhi). Kuma ManzanAllah Sallallahu Alaihi Wasallam yace:(“kadakurigayi ramadana da Azumin kwana dayake kwana biyu in banda mutumin da yakasance yanayin wani Azumi to se ya Azumceshi” Muslim)

Wallahu A'alam

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*

Post a Comment (0)