MAGANIN ƘANƘANCEWAR NONO


*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_*

_*Daga zauren*_
_*📌 Albahral Ilmu 🌴*_
.
.
*_MAGANIN ƘANƘANCEWAR NONO :_*
:
*_TAMBAYA_*
:
_Malam dan Allah tmbyata anan itace shin meke janyo kankancewar nonuwa ajikin mace kuma dan Allah idan akwai abinda za'iya yi dan mangancewa faruwar haka toh malam dan Allah ataimaka min dan na rasa yadda xanyi. Nagode. Kuma dan Allah malam a boye sunana._
:
 _*AMSA*_
:
_Dalilan da suke kawowa Qankancewar nonuwa ajikin mace, suna da yawa. Amma mafiya faruwa daga ciki sune:_
 _*(1).* Jinya mai tsanani (musamman adaidai lokutan farkon balaga)._
.
_*( 2).* Gadon dangi: idan ya kasance yawancin matayen danginki kamar mahaifiyarki, kakarki, ko Goggonki suna da irin wannan yanayin, to kema hakan zai iya shafarki._
.
_*(3).* Yawan amfani da Kwayoyin rage Qiba. Ko kuma magunguna ba bisa Qa'ida ba._
.
 _*(4).* Sirantaka: Idan ke siririya ce sosai, to nonuwanki zasu iya xzama Qanana. Domin kuwa Kitse ne yake taruwa aduk guraren bambancin halitta tsakanin Mata da maza. Kamar nonuwa, mazaunai, kutiri, etc._
.
 _*(5).* Adaidai lokacin balaga, Akwai wasu sinadai na kwayoyin halitta wadanda jikin mutum yake fitarwa. Wani lokacin kuma, ana samun matsalar ne idan jikin mace ya kasa fitar da isassun hormones din da zasu gabatar da wannan aikin._
.
 *_MAGANI_* 
_*(1).* Ki samu garin Hulba ta asali marar gauraye. Ki rika zuba cokali 2 acikin kofi guda na madarar shanu. Ki gauraya ki shanye kullum.... Tare da sugar ko zuma. Amma fa BA MADARAR KANTI BA._ _Sabuwar madarar shanu nace.. Idan baki samu ba, ko nonon akuyarki ko Tinkiyarki ki tatsa kiyi dashi._
 .
_*(2).* Ki samu man hulba original (made in egypt ko Saudia ko Syria) ki rika shafawa a nonuwan naki. Insha Allahu zakiyi mamaki sosai._
.
 _*(3).* Ki yawaita cin kitse acikin abincinki (musamman ma. Vegetable fat). Wallahu a'alam._
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
_*©​​✍🏽 ​​Abdulkadeer Umar Alshinkafawy*_
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*--------------------------*
*_​•Ga mai sha'awar shiga Zauren *📌 *Albahral Ilmu*🌴
_*​ta whatsApp sai yayi cikakkiyar sallama tare da suna da Address nasa zuwa⬇ ga lambar mu*_​​​​   
      _*07064746551*_
 _*07032076804*_   
〰〰〰〰〰〰〰〰〰
Post a Comment (0)