MUGUNTA BA TA DA RIBA


MUGUNTA BA TA DA RIBA 

Watarana wani Kyarkeci ya fita neman abinci. Yana ta tafiya har ya isa wani ƙauye da ke ƙarshen dajin da yake. Kwatsam sai ya yi arba da ayarin wasu tumakai suna kiwo. Yana nan yana tunanin yadda za a yi ya kama ɗaya ya cinye sai ya ga wata fatar tunkiya a yashe gefen hanya. Nan take sai wata muguwar shawara ta zo masa. 

Sai ya yi tunanin bari ya sanya wannan fata a jikinsa, saboda yin hakan zai ba shi damar shiga cikinsu ya yi ta'asa cikin sauƙi. Kyarkecin na isa ayarin waɗannan tumakai, sai makiyayin da ke kiwonsu ya kaɗa su suka nufi gida. Da suka isa gida kuwa ya sa su a ɗaki ya kulle. Ya fito kenan sai matarsa ta ce, "Mai gida, yau fa ba mu da abincin dare, me zai hana ka yanka mana tunkiya ɗaya mu dafa?" Mai gida ya yi na'am da wannan batu, don haka sai ya koma ɗakin tumakan da nufi ya kamo ɗaya ya yanka, bisa sa'a kuwa sai ya kamo wannan Kyarkeci ya yanka shi. 

Ƙarshen labarin kenan. 

Darasin Labari: Ita mugunta ba ta da riba. A duk lokacin da ka nufi yi wa wani mugunta to kanka ka ke yi wa. Dubi dai yadda rayuwar wannan Kyarkeci ta salwanta a garin yin mugunta. Allah tsare mu. 

Mu so junanmu, domin junanmu. 

Kyakkywan tunani, kyakkywar rayuwa. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
Haimanraees@gmail.com



Post a Comment (0)