ABUBUWAN DA AKE DUBAWA WAJEN ZABEN MIJI
https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum
Malam dan Allah wayanne abubuwa ake dubawa a wajen zaben Mijin da za'a aura?
*AMSA*👇
ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،
Yar uwa idan kika tashi zaben Mijin ki toh yanada matuqar muhimmanci ki natsu ki duba wadannan ababe a tattare da wanda zaki zaba ya zama Uban 'ya'yan ki na har abada. A lokacin zaben Miji ana so mace ta duba ababe kamar haka:
*1. Addinin sa da dabi'un sa.*
Wannan shine Abu na farko da ake dubawa ga namiji idan yazo Neman auren mace. Wajibi ne ya kasance musulmi Wanda yake kokarin kiyaye dokokin Allah kuma yake bin karantarwar musulunci a rayuwar sa ta yau da kullum.
Ya zama wajibi akan Waliyin mace yayi bincike akan addinin sa da dabi'un sa sosai akan Wanda ke Neman auren ta, kar a dogara akan halayensa na zahiri kawai. Kuma Abu mafi muhimmanci da za'a bincika shine yanayin rikon sallar sa, domin duk Wanda ya kasa rike haqqin Allah na sallah, toh bazai iya kiyaye haqqin mace ba idan ya aure ta.
Namiji mai tsoron Allah mai riko da addini da dabi'u nagari bazai tsangwami matarsa ba, kuma bazai cutar da ita da komai ba. Idan yana sonta zai yi mata adalci ya kyautata mata, idan kuma baya sonta toh bazai cutar da ita da komai ba kuma zaiyi mata adalci, domin yana tsoron haduwar sa da Allah. Shiyasa *Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa sallam)* yake bayyana mana cewa idan mutumin da muka yarda da addinin sa da dabi'un sa yazo neman wacce take karkashin kulawar mu, toh mu aura masa ita (matuqar tana sonsa).
*2. Namiji Mai tausayin mace.*
Yana daga cikin ababen da mace zata duba ga namijin da take muradin ya zaman abokin rayuwar ta shine _"Mai tausayin mace"._ Saboda yazo a hadisin da *Muslim* ya kawo mai lamba 1480 cewa *Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Sallam)* yace wa *Fatimah bintu Qays (radiyallahu anha)* a lokacin da ta nemi shawarar sa akan mazaje uku da suke neman auren ta, sai Manzon Allah yace shi *Abu Jaham* bulalar sa bazata taba rabuwa da kafadar sa ba (yana nufin *Abu Jaham* yana yawan dukan mata).
*3. Lafiyar sa.*
Yanada kyau mace ta bincika lafiyar Namijin da zata aura. Idan yanada lafiyayyen jiki, kuma baya yawan rashin lafiya, bashida nakasa, kuma shi ba juya bane, yana haihuwa, domin ba'a auren Wanda baya haihuwa, kuma baya dauke da wasu kwayoyin cuta a jikin sa. Shiyasa malaman wannan zamani suka bada fatawar halascin zuwa asibiti a bincika lafiyar wadanda suke nufin yin aure kafin ayi auren. Domin kaucewa aikin dã-nã-sani.
*4. Aikin yi ko Sana'ar sa*
Yana daga cikin ababen da mace zata duba ga namijin da yake son auren ta, a bincika aikinsa ko sana'ar sa. Domin daukar dawainiyar mace tin daga ciyarwa, shayarwa, tufatarwa da kula da lafiyar ta yana rataya ne a wuyan Mijinta idan ya aure ta. Saboda haka dole ne a duba agani idan yanada rufin asirin da zai iya yi mata wannan hidima ba tareda ta roki mutane ba ko ta nemi ayi mata hidima daga gidan su ba. Anan fa ba ana nufin sai Namiji mai kudi ba, a'a mai rufin asiri Wanda zai hana kansa da iyalan gidansa roqon mutane. Saboda *Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Sallam)* yace wa *Fatimah bintu Qays (radiyallahu anha)* _"Shi Mu'awiya tareeb ne (faqiri talaka kenan) Wanda bashida dukiya."_ _*(Muslim, 1480)*_ Anan ba wai ana nufin dukiya mai yawa ba, ana nufin bashida abinda zai iya riqe kansa da matar sa dashi.
Kuma shi wannan binciken na sana'ar mutum ko aikinsa yanada matuqar muhimmanci domin a tantance cewa ba da dukiyar haram zai ciyar da ita ba.
*5. Mai Ilimin Qur'ani da Sunnah.*
Yafi dacewa idan akwai mai qãrin darajar ilimin Qur'ani da Sunnah cikin masu neman auren ta, ta zabi Wanda yafi su ilimin Qur'ani da Sunnah idan dukan su sunyi kunnen doki a sauran ababe. Amma kuma ki lura da cewa masu irin wannan sifa yan kadan ne cikin al'ummah, saboda haka kar ki ce dole sai kin samu irin sa. Akwai masu taqwa sosai amma kuma basuda zurfin ilimi sosai.
*6. Shin yanada manya masu taka masa burki.*
Yanada muhimmanci mace ta binciki namijin da ke neman auren ta, shin yana jin maganar manya? Akwai masu taka masa burki idan ya aikata ba daidai ba? Ko dai yafi karfin kowa? Wannan ma Abu ne mai muhimmanci da ya kamata a bincika akan mai neman aure.
*7. Istikhaarah.*
Yanada kyau yar uwa idan kika auna wadannan ababe akan mai neman auren ki, toh kiyi istikhaarah ki barwa Allah zabi. Kowa shi yake yiwa kansa istikhara kamar yadda wani bazai yiwa wani sallar farillah ba. Haka sallar istikhaarah take.
Mai neman karin bayani ya ziyarci wannan littafi:
_*Jaami’i Ahkaamun Nisaa’a na Shaykh Mustafaa al-‘Adawi.*_
جامع أحكام النساء للشيخ مصطفى العدوي مع زيادة.
Daga karshe yan uwa mata da maza ina mai bamu shawarar muyi kokarin zama mutanen kirki idan muna fatan samun abokan rayuwa nagari. Domin Mata nagari saboda maza nagari suke, haka maza nagari saboda mata nagari suke. Kamar yadda wasu malaman tafsiri suka bada tafsirin wannan ayar....
الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ ۖ وَالطَّيِّبَاتُ لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَاتِ ۚ .......
النور (٢٦)
_Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke......_
_*(Suratun Nuur, Ayah ta 26)*_
Muna rokon Allah ya hadamu da abokan rayuwa nagari wadanda zamu samu Aljannah a dalilin auren. Masu aure acikin mu Allah ya kara hada kansu, ya kuma daidaita tsakanin su yasa Aljannah ta zama sakamakon auren su.... Amin yaa Hayyu yaa Qayyum.
والله أعلم،
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*