HANYOYIN DA YA KAMATA MU BI DOMIN ZABEN MACEN AURE



HANYOYIN DA YA KAMATA MU BI DOMIN ZABEN MACEN AURE

Yawan rabuwar aure a kasar Hausa abu ne da ya yi kusan zama Ammatul Balwa, (abinda kusan kowane sako da lungu zaka iya samun irin wannan matsalar na faruwa). To amma meke janyo irin wannan matsalar?

Rashin zabar mace ko namiji mai 'dabi'un kwarai da addini shine farko daga cikin musabbabin faruwar wannan lamari (Na rabuwar Aure).

Abu Aswadu na daga cikin magabata ya taba cewa, ‘ya’yansa “Hakika na kyautata maku yarintar ku da tsofar ku, tun kafin a haife ku!” Sai suka ce, “Yaya ka kyutata mana tun kafin a haife mu?” Sai ya ce, “Na zaba maku uwar da ba za ku zarge ta ba (wato ba za ku kushe ta ba). Kenan zaben mace mai kyawawan dabi'u na daga cikin abubuwan da ke taimakawa zaman aure.

Wani bawan Allah ya je wajen Hasanul Basri ya ce, “Ina da ‘ya wacce nake son ta, jama’a da yawa suna sonta. Wa zan aurarwa? Ba ni shawara?” Sai Hasanul Basri ya ce, “Ka aurar da ita ga mai tsoron Allah idan yana sonta. Sai ya karrama ta. Idan kuwa ba ya son ta ba zai zalunce ta ba.” (saboda tsoron Allan sa). Kenan ko mata ya kamata su lura sosai da sosai awajen zaben mijin aure domin gujewa Rabuwar aure tunda ko baya sonta zai karramata.

Haka ma wani mutumi ya kai karar dansa wajen Sayyidi a Umar ibn Kaddab (RTA) yake cewa, Ya Amirul Muminina dana ba ya yi min biyayya. Sai Sayyidina Umar ya sa aka kira dan ya yi masa nasiha ya tsorartar da shi illar rashin yi wa iyaye biyayya. Daga nan sai yaron ya ce wa Sayyidina Umar, “Shin su ma ‘ya’ya suna da haqqi a kan mahaifansu?” Sai Sayyidina Umar ya ce, “Eh akwai!” Sai yaron ya nemi a yi masa bayani.

A nan ne Sayyidina Umar ya ce, “Na farko uba ya zaba wa ‘ya’yansa uwa tagari kuma ya sanya masa suna kyakkyawa. Sannan ya koyar da shi littafin Allah. Da wannan yaro ya ji haka sai ya ce wa Sayyidina Umar “Babana bai yi min ko daya ba. Babana da ya tashi yin aure bai auro mani uwa tagari ba. Babana ya auro mana karuwa ne daga cikin karuwan Maguzawan kasar Sudan.

Kenan rashin auren mace mai kyawawan dabi'u ba mutuwar aure kawai yake kawowa ba, har tarbiyar yara yana lalatawa.

Wannan shi ya zaburar da ni domin in nunawa 'yan uwa wasu hanyoyi da za su taimaka musu domin samun mace ta gari. Ko rabuwar aure za ta yi sauki a kasar Hausa.

Baya ga haka kuma Manzon Allah (SAW) ya bayyana mana dadin duniya, kuma ya nuna cewar mafi alkairin dadinta shine: Mace tagari; inda yake cewa, duniya dan jin dadi ne, kuma mafi alkairin dadinta shine: mace tagari.

A wata ruwayar kuma ya ce, duniya dan jin dadi ne, kuma babu wani abu daga mata'in duniya wanda ya fi mace tagari. Kenan samun mace ta gari ba karamar riba ba ce a wannan rayuwa.

Da farko yana daga cikin hanyoyin zaben macen aure, shine binciken halayen mahaifan yarinya shin masu tarbiya ne ko kuwa? Kuma ka sani muddin ka ga mahaifiyar ce ke mulkin gidan ba mahaifin yarinyar ba, to kuwa akwai matsala. Ka guji auren yarinyar gidan.

Domin Idan ka auro yarinya a gidan da ba su da tarbiyya ‘ya’yanka zasu zama marasa tarbiyya. Shi ya sa yana da kyau mutane su kula da kyau wajen aure domin ‘ya’ya suna biyo iyayensu mata ne.

Bayan wannan kuma musulunci ya yarda kasa a bincika maka Yarinyar ita kanta, Shin Salihace a zahirce ko kuwa? Kuma abincika maka ko mai gaskiya ce, ba makaryaciya ba, Shin tana cika sallolinta, da azumi, Shin mai kiyaye farjinta ce daga alfasha?

Muddin ta kasance da wayannan halaye to itace maccen da ya kamata ka Aura domin a wani hadisin Manzon Allah (SAW) ya nuna mana cewa, Mace ba za ta lazimci wadannan aiyukan ba face sai ta shiga aljanna.

Abu na gaba da ya kamata Samari su lura da shi a wajen Aure shine kada su auri Bazawara. Domin yanzu zaka ga saurayi bai taba aure ba yazo ya auri bazawara wanda kuwa ba karamar matsala yake haifarwa ba a gidan ma'aurata.

Domin Manzon Allah (SAW) ya ce, “Na hore ku idan zaku yi aure ku auri ‘Yammata’ (budurwa) domin mahaifarsu ta fi tsafta kuma bakinsu ya fi dadi kuma suna yarda da dan kadan.”

Amma fa ba nace bai halatta ba, su ma zawarawan akwai alheri,
sai dai ba su kai ‘yammata
Post a Comment (0)