ALKALAMI SHI NE FARKON ABIN DA ALLAH YA HALITTA, BA HASKEN MANZON ALLAH KO ZATINSA BA
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
*TAMBAYA*❓
Assalamualaikum malam Ina maka fatan alkhairi.
Inada tambaya kamar kaha; Naji wani malami yana cewa "lokacin da ubangiji ya warzu farkon abunda ya fara halitta shine manzon Allah (s.a.w)". Ina son Karin bayani akan haka. Sannan Ina son Karin bayani akan kalmar WARZUWA?
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Wajibi ne Al'ummar Musulmi su nisanci gurbatattun aqiidu, da munanan ayyuka, duk abin da za su kudurta na Aqiidah to su tabbatar da cewa bai saba wa Alkur'ani da Sahihan Hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah ba, duk abin da za su aikata na wani aiki to su tabbatar da cewa bai saba wa Alkur'ani da Sahihan Hadithan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba. Yin haka shi ne samun nasararsu Duniya da Lahira.
Imam Abu Daawuud ya ruwaito hadithi na 4,702, da Imamut Tirmizi hadithi na 2,155, da Imam Ahmad hadithi na 22,757 daga Sahabi Ubaadatu Dan Saamit, haka nan ma Imamul Haakim cikin Mustadrak dinsa hadithi na 3,693, da Imamut Tabaraanii cikin Almu'ujamul Kabeer hadithi na 12,060, da Imamul Baihaqii cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 18,157 daga Sahaabi Abdullahi Dan Abbas, sannan Imamul Albaanii da sauran masana Ilmin Hadithi sun inganta shi, dukkan wadannan Sahabbai biyu ko wannensu ya ce:-
((Na ji Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana cewa: Lalle farkon abin da Allah Ya halitta shi ne Alkalami, sannan Ya ce da shi: Ka rubuta, to sai ya ce: Ya Ubangijina mene ne zan rubuta? Sai Ya ce: Ka rubuta kaddarorin kome har Sa'ah ta tsaya)).
Kamar yadda kuke gani wannan nassi ne na sahihin hadithi, to amma kuma duk da haka sai ga shi Aluusii ya hikaito daga Sufaye cikin tafsirinsa mai suna Ruuhul Ma'aanii 17/105 cewa sun ce ya zo cikin Hadithi cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce wa Sahabi Jabir Dan Abdullahi :-
((Ya Jabir! Farkon abin da Allah Madaukakin Sarki Ya halitta shi ne hasken Annabinka)).
Don Allah ku duba ku ga irin yadda Sufaye suka bar yin aiki da ingantaccen hadithi, suka koma suka kirkiro wani hadithin karya suka jingina shi zuwa ga Annabi mai tsira da amincin Allah, ta inda kuwa za ku fahimci cewa hadithin na karya ne shi ne: Sam ba ya rubuce cikin littattafan hadithi sanannu, wannan shi ya sa ma a lokacin da Sheik Muhammad Jameel Zainu yake bayanin hadithai na karya cikin littafinsa mai suna: Minhaajul Firqatin Naajiyah Wat Taa'ifatil Mansuurah shafi na 74 ya ce:-
((Ya Jabir! Farkon abin da Allah Ya halitta shi ne hasken Annabinka". maudhuu'ine)).
Shi ma Sheik Albanii a cikin littafinsa Silsilatul Ahaadithis Sahiihah 1/457 a lokacin da ya kawo hadithin nan na 2,996 da Imam Muslim ya ruwaito cikin Sahihinsa watau:-
((An halicci Mala'iku daga wani irin haske ne, sannan an halicci Aljannu daga wani irin harshen wuta mai launin baki-baki ne, sannan kuma an halicci Adamu ne daga abin da aka siffanta muku)).
Sai ya ce:-
((Cikin wannan hadithin akwai isharar cewa hadithin nan da ya shahara cikin harsunan mutane, watau: "Ya Jabir farkon abin da Allah Ya halitta shi ne hasken annabinka" da ma irinsa daga cikin hadithan da suke cewa: Annabi mai tsira da amincin Allah an halicce shi ne daga wani irin haske magana ce ta karya. Lalle wannan hadithin hujja ce karara da ke nuna cewa: lalle Mala'iku ne kadai aka halitta su daga wani irin haske, amma banda Adamu da 'ya'yan shi. Sai ka fadaka, kada ka kasance daga cikin gafalallu)).
Allah Ya shiryar da sufayen cikin wannan Al'ummah, Ya kuma nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.
Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*