WAI BATA IYA BACCI ITA KAƊAI
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
*TAMBAYA* ❓
Aslmk mal Allah ya kara lfy, mal mutum ne yayi amarya to sai taxo da wani salo wai ita bata iya bacci ita kadai sai da mutum a dakin, sai tayi ihu wai tana firgita saidai axo falo axauna indai ba ranar kwananta bane, to shine mal mijin ya yanke shawara cewa duk kansu xasu ringa kwana a dakin shi kawai Amma za a kashe wuta karwata taga tsaraicin wata mal hakan ya hallarta.
*AMSA* 👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Da Ace Shine ya Nemi Shawara sai Ince masa. Abinda ya Kamata Shine, ya Samar Mata Wadda Zata ke taya ta Kwana Idan ba a dakinta yake ba.
Amma idan a dakinki yake bai kamata a yi haka ba. Sabida babu Nutsuwa gaskiya.
Ma'ana idan yana dakinta zasu kwanta tare, Sabida ta sami Wanda zasu Kwana tare. Mijinta Kenan. Idan kuma yana dakinki sai ta zo Ku kwana tare a dakinsa. Sabida na san Nan Gaba zasu zo Miki da Wannan Tsarin. Idan har Sun Latsa sun ga Ta kai Musu.
Amma duk da Haka Ki Bashi Shawara ya Samar mata wadda zatake taya ta Kwana. Ko da yarinyarki ce tana taya ta Kwana. Ko kuma daga Makotanku ne ko wata Yar uwarsa ko kuma Yar Uwarta.
Amma. Rabon Kwana Wajibi ne ga wanda yake da Macen da ta Wuce guda daya.
Allah Shine Masani.
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕