SHIN ANNABI MUHAMMAD NE FARKON HALITTA❓

SHIN ANNABI MUHAMMAD NE FARKON HALITTA❓ 

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu alaikum Malam

Ina da wata tambaya wacce ta daure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka bani tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Annabi Muhammad ne Allah ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shine sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?

 *AMSA* 👇

Wa'alaikum assalam, Akwai hadishin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi ? shi ne farkon wanda aka fara halitta, saidai hadishin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin karya ne.

Fadin cewa Annabi ? shi ne farkon wanda aka halitta ya sabawa alqur'ani, ta bangarori da dama ga wasu daga ciki:

Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad ? mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba daya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi MUHD shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin alqur'ani.
Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad ? tun daga mahafinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.
Zance mafi inganci shi ne: farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa: "Allah ya kaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa"

Kin ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi Muhammad ?.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕


Post a Comment (0)