ƊAUKAR NIYYAR AZUMI


ƊAUKAR NIYYAR AZUMI 


*”Niyyar Azumi”*
Niyya shine abinda ka qudurta zaka aikata acikin zuciyarka,Niyya muhallinta a zuciya yake,furta niyya da harshe bidi’ane ko da mutane suna ganin yin hakan shine daidai awajansu,amma bidi’ane saboda bai tabbata ba daga Manzon Allah SAW.

A-Wajibine mutum ya dauki niyyar azumin Farilla idan ya sami labarin ganin wata kafin fitowar alfijir,saboda fadan Manzon Allah SAW

*(Dukkan wanda bai daura niyya Azumi ba da dare kafin fitowar alfijir,to baya da Azumi)*
@Abu Dauda Da Ibn Khuzaima.

*(Dukkan wanda bai kwana da niyyar azumi kafin alfijir ya fito ba,to baya da azumi)*
@Nisa’i da Tirmizy


*”Wanda bai sami labarin ganin wata ba har sai da gari ya waye”*

Wajibi ne ka daura niyyar yin azumin
Ramadan tun da dare kafin fitowan Alfijir.

Wanda bai sami labarin ganin wata ba sai ya zamanto ya tashi ba ya azumi idan ya samu
labari(ko bayan Sallar la’asar ne sai ya yi niyyar azuminsa a wannan lokacin ya daina cin abinci, kuma azuminsa ya yi, don haka ba zai rama ba(amma fa ba a ce mutum ya shantake ba)
@Nayl Autar da Sifatus Saumin Nibiyy

Sheihkul Isam ibn Taymiyya shi da Dalibinsa ibn Qaym sunce azuminsa nanan babu komai a
gare shi azuminsa yayi basai ya rama ba.
@ Majamu’ul fatawa 109/25 da Zadul ma’ad 74/2 @MuktaraatulJalila na ibn Sa’adi 60 .

Wannan mas’alace mai sabani mai yawa awajan Malamai,amma abinda yafi inganci shine abinda yazo a littafin:
“صفة صوم البي صلي الله عليه وسلم”
*”Wanda bai sami labarin ganin wata ba na Ramadhana har sai da gari ya waye,har yaci abinci bai sani ba,ko bai ci ba,idan ya ci abinci to ya kame daga cikin cin abincin,kuma ya cikasa azuminsa,amma idan bai ci ba to kada yaci yaci gaba da azuminsa,kuma azuminsa yayi ba sai ya ramaba*”

Saboda da dalilai kamar haka-
*”Yana cikin Qa’idodin shari’ar musulinci cewa:Ana wajabta maka abune idan kana da iko kuma kana da dama kuma ka riske lokacin”* shine suke cewa:
*القدرة مناط التكليف*
Wanda bai sami labarin wata ba har sai da gari ya waye ai baya da ikon dauren niyya cikin dare,ikonsa anan shine zai dauri niyya alokacin da labari ya riskesa.

Na biyu:
Daga A’isha R.A tana cewa:
*”Manzon Allah s.a.w ya kasance yana umarni da Azumin Ashura,lokacin da aka wajabta Ramadhana,sai ya kasance wanda yazo ya azuminci ashura sai yayi Azumi,wanda baiga ba dama sai yakiyi”*
@Bukhari da Muslim

Daga Salmata Bn Akwa’in R.A yana cewa:
*”Annabi S.a.w yana umarnin wani mutum daga cikin musulmai yayi shela ga mutane cewa wanda yaci abinci ya kame yaci ba da Azuminsa,wanda kuma bai ci ba kada yaci yaciga da azumi yaune ranar Ashura”*
@Bukhari da Muslim

Da Azumin ashura shine farilla kuma da aka wajabta Ramadhana sai ya tashi daga wajibi ya koma mustahabbi,tun har ana umarnin wanda yaci yaciga da azumi aranar Ashura,to haka shima hukuncin yake awatan Ramadhana
@Siffatus saumun Nabiyy shafi na 31

Allah ne mafi sani

*Ya Allah ka isar da rayuwar mu watan Ramadhana muna imani da kyakkyawar niyya*.
Post a Comment (0)