HUKUNCIN GAISUWAR SHIGA WATAN RAMADAHA:
Daga Abi Hurairata R.A yace:
"Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yiwa Sahabbansa albishir da shigowar watan Ramadhana,yana cewa masu”-
*(Hakika watan Ramadhana yazo maku watane mai albarka,Allah ya wajabta maku yin azuminsa,acikinsa ake bude kofofin aljanna kuma ake rufe kofofin wuta,kuma a daure shaidhanu,acikinsa akwai wani dare da yafi alkhairi akan daren watanni dubu,wanda aka haramta masa samun alkhairin wannan wata hakika an haramta masa alkhairi)*
@صحيح الترغيب 1/490
الحافظ ابن رجب رحمه الله تبارك وتعالى:
Yana cewa:
*Wani sashe daga cikin malamai suna cewa,wannan Hadisi jigone kuma asaline daga cikin hujjar mutane suyiwa junansu gaisuwa da murar shigowar wannan watan na Ramadhana,mi zai hana mai imani bazayi farinciki ba tare da albishin ga dan uwansa ba saboda a watane ake rufe kofofin wuta baki daya a bude kofofin aljanna baki daya,a daure shaidhanu…….*
@لطائف المعارف (1/158)
Dan haka ya halasta yin gaisuwa ga juna dan shigowar watan Ramadhana Mai albarka.
Allah ne mafi sani.