BANBANCIN MACE MAI AURE DA MARASA AURE
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
*TAMBAYA* ❓
Malam ina da tambaya akan macen da ta dade batayi aure ba,tabbas nasan komai sai lokacin da Allah yayi yake faruwa,amma sai naji wasu suna cewa tayi wasa da damarta,Dan Allah ayimin bayani sosai malam, jazakumullahu khaira.
*AMSA* 👇
Eh Tabbas haka ne. Duk Matar da take Zaine ba Miji An sha da ita Gaskiya.
Domin Akwai Babanci Sosai a tsakanin Mace Mai Aure da Maras Aure.
👉 Na Farko Akwai Saduwa ta Auratayya. Wanda wannan wani jin dadi Ne da wadda bata da Aure ta Rasa. Idan Sha'awarta ta ta Motso Mata sai dai Kawai ta kama juyi akan Gado. Sai dai ko idan Zina Zatayi da wani ko ta Kalli fina-finan Turawa na Batsa ta rararrage. Wanda kuma Bala'ine Mai Zaman Kansa. Domin Mai Kallon Blue Film Na Banza Akwai Azabar Allah. Sannan kuma yana sanya Makanta.
👉 Haka zalika Akwai dauke Kewa wadda mai Miji take samu, Domin Mijinta Shine Abokin Shirarta da yawonta da Sauransu, kwana Da Namiji a Kusa da ita, Kokarin Birge Wannan Mijin Nata da dai Sauransu. Ba zasu Kirgu ba.
👉 Akwai Mu'amula da dangin Miji da Yan Uwansa da Kyakykyawar Alaka a Tsakanin yan Uwanta da yan Uwanki Mijinta. Musamman Ma Masu Aure. Sabanin Maras Aure zakiga Kawayenta Yan Mata ne. Komin Shekarunta ba Aure. To fa sai dai ki ganta a cikin Yara Yan Mata. Domin Sune Kawayen. Sune Abokanan Huldarta.
👉 Ita Kanta Mai Miji ta fi Baiwa Kanta da kanta Kulawa. Sabida ta sani Akwai Wanda zata Birge. Ko da kuwa ba zai yaba Mata akan Wannan Kwalliyar ba.
👉 Mace mai Miji komai yimata akeyi ga Wadanda suke san Hakkin Aure. Maras Miji Kuma sai dai da kame-kame. Kai ko Iyayen mace mai Miji da danginta sunfi kyautata mata a lokacin da take Gidan Auren ta. Sabanin wadda take gidan su. Kullum fada da Yan Uwanta, Wani lokacin ma da Iyayensu Suke yin Fada.
👉 Mai Aure a koda yaushe idan an ganta ta fi Kima da Mutunci a idon A'umma. Sabanin Maras Aure. Kowa mq zai Iya Latsa ta. Kowa ma zata Iya gani a wajen ta. Wanda ya dace da wanda bai dace ba.
👉 Mace Mai Aure zaka samu Tana Haihuwa. Wanda a Duniya da Lahiri Manzon Allah saw Zaiyi Alfahari da Wannan Abinda Suka Haifa. Maras Aure kuwa ba Haihuwa. Ko da kuwa ta Haihu ba Aure. Manzon Allah saw ba Zaiyi Alfahari da wannan Haihuwar ba.
👉 Mai Aure tana Samun ladaddaki Na Musamman a Gidan Aurenta. Maras Aure kuwa. Me take samu. Manzon Allah saw Yace "IDAN MACE TA KIYAYE SALLOLIN TA GUDA BIYAR, TA KIYAYE AZUMINTA NA RAMADAN, TA YIWA MIJINTA BIYAYYA. ZATA SHIGA ALJANNAR UBANGIJINTA. Wannan Falalalar kadai ta kebanta ga Mace mai Aure. Banda Maras Aure.
Atakaice kenan. Amma Maganar gaskiya Banbancin Ba zai Kirgu a nan ba.
Banbancin Kamar Banabancin Nisan Sama da Kasa Ne. Sannan ba zai Rubutu anan Ba.
Duk da Cewar da Akasarin Matan Wannan zamanin Idan sun Samu Mazajen Auren, Renawa Suke yi.
Amma dai wadda take son Auren Rufin Asiri. Ba Auren Neman Abin Duniya ba. Allah ya kawo Mata na Gari.
Allah shine Masani.
KU TAYA MU ISAR DA WANNAN SAKON TA HANYAR SHARING, WASU DA YAWA ZASU AMFANA.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*