HUKUNCIN MATAR DA TA RIKE YARA MARAYU



HUKUNCIN MATAR DA TA RIKE YARA MARAYU

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu Alaikum, malam da fatan kana lafiya tare da iyalan gidanka amin.

Malam tambaya ta itace akwai zunubi ne ga matar dabata wuce aure ba kuma taki tayi sabida yara marayu da baban su ya rasu ya bari tsawon shekara 4? sakamakon ba mai kula dasu da tarbiyyar su kuma yara har 8 ba mai auren ta da wadannan yara.naji wasu nacemin ai Allah yasan da zaman kowa yin aure yafi zama ba aure.na gode da amsa min tambayata da zakayi malam..


 *AMSA* 👇

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Babu wani laifi akanki mutukar dai kina iya kiyaye mutuncin kanki, Kuma kinyi hakan da kyakkyawar niyyah.
Shi kansa rikon yara marayu da bayar da tarbiyyah garesu, ibadah ce mau zaman kanta. Kuma Manzon Allah (saww) ya fa'di falalar wannan din acikin hadisai da dama.
Babu laifi ga matar da aka mutu aka bar mata yara Qanana Marayu, ta zauna waje guda tare dasu ta
kula da tarbiyyarsu kamar yadda addinin
Musulunci ya koyar. Kuma zai fi kyawu gareta koda auren zatayi ta rika hangen maslahar yaranta. Da kuma yadda rayuwarsu da tarbiyyarsu zata
kasance. 

WALLAHU A'ALAM.

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)