BIN LIMAMI SALLAR JAM'I DAGA GIDA
https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
*TAMBAYA*❓
Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu,
Allah ya Kara wa mallam hirsi da imami da arziki da wadata,
Tambaya :
1.Ya halasta ga mace ko namiji su bi limami salla acikin gida ko ofis, ta speaker.
Wafakumullahu ya sheikul islaam
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Wa iyyakum brother. Amma amsar wannan tambaya ta gabata, a takaice baya halatta wani yayi koyi da liman a gida ta lasifika ko kuma ta sautin shi dake isowa a gida ko shagon mutum na kasuwa.
Baya halatta ga mace ko namiji ya bi sallar jam'i daga gida, saboda abin da Annabi yace da makaho na, yana jin amon sautin kiran sallah daga gidan sa, yace eh, sai yace, toh ka halarci sallah, bai ce ya zauna gida ya bi liman ba.
" هل تسمع النداء بالصلاة ؟ " قال نعم ، قال : " فأجب " أخرجه مسلم في صحيحه .
Bayan wannan kuma Annabi yace a wani hadisi wanda duk ya ji kiran sallah bai zo masallaci ba, toh baya da sallah (cikakkiya) sai saboda wani uzuri.
" من سمع النداء فلم يأت فلا صلاة له إلا من عذر " أخرجه ابن ماجه والحاكم
Don haka ɗayan biyu ne, ko dai mutum, ya je masallaci yayi koyi da liman ko kuma yayi sallar shi a gida shi kaɗai ko da iyalin sa. Amma hadisin da yake cewa babu sallah ga maƙwabcin masallaci, wannan hadisi bai inganta ba. Shaikh Bn Baaz ya raunata hadisin da aka yi masa tambaya
الحديث ضعيف، لا صلاة لجار المسجد إلا في المسجد ضعيف
Amma babu laifi, idan sahu ya zo har ƙofar shago ko gidan mutum, yayi sahu tare da sauran mamu don yayi koyi da wanda yake koyi da liman.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕