KA HAKURA BA GIDANKA BA NE


KA HAKURA BA GIDANKA BA NE!!!

Kyan kama, da kyawun gidaje, da kyawun kayan ado, da burgewa wajen iya magana duk sun sha gabanka.

Allah Yana cewa: " Idan ka gansu, jikinsu ma zai ba ka sha'awa, Idan suka yi magana za ka saurari maganarsu...". Munafikun: 4

Ya Kuma ce: " Kafirai suka ce wa muminai: A cikin bangarorin nan biyu (Musulmi da Kafirain) wa ye ya fi matsayi mafi kyau, kuma ya fi kyawun majalisa? ". Maryam: 73

Na farko bayanin munafukai ne, na biyu kuma Kafirai.

Kai kuwa an gaya maka daga baki Mai daraja:

"Duniya kurkukun mumini ce, kuma aljannar kafiri ce".

Saboda haka kada ka zake da yawa, kada ka yi kukan zuci, ka yi shiri Mai kyau don za ka koma gidanka na asali wanda babu kamarsa.

Mu nemi dacewa a komawarmu.


Daga
Miftahul ilmi

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)