DA ME ZA MU FUSKANCI RAMADAN? 01

**DAME ZA MU FUSKANCI RAMADAN ??* 
                     *001* 
بسمالله والصلاة والسلامعلى رسول الله وعلىآله وصحبه أجمعين
Bayan sanya sunan Allah, da salati ga Fiyayyen Halitta da Alayensa da 
Sahabbansa baki daya, Bayan haka.
“Yan Uwa taken wannan rubuta nawa shine DAME ZA MU FUSKANCI 
RAMADAN ???
Wannan wata muhimmiyar tambaya ce da ya kamata ace kowane Musulmi ya 
tambayi kansa, domin yin tanadi ga zuwan wannan wata mai alfarma da 
daraja.
Magabata na qwarai koda yaushe babban abin dubinsu shine Gobensu 
(Qiyama) shi yasa suke shiri domin riskuwarta ta hanyar zage damtse wajen 
yin Ibadodi.
Sahabbai sun kasance dayan su kanje kasuwa yayi dako a biyashi ba domin 
ya ci ba, sai don kawai ya kawo Sadaka wajen Manzon Allah (SAW). Wannan 
na nuna mana yadda sahabbai suke da kwadayin Lada.
Mu kuma ayau babban abinda muke duba duniyar nan kadai, shiyasa mafi 
yawancin mu babu wani tanadi da muka yiwa Goben mu. Babban fádi táshin 
mu akan lamurran duniya ne kawai.
DAKATA KAJI WANNAN LABARI
A shekaru uku zuwa hudu da suka gabata wata babbar Supermarket ta 
shelanta za ta saki garabasa (Bonanza) inda ta ayyana rana da lokaci, ta 
sanya sharadin garabasar shine za‟a ba da daqiqa (minti) daya duk abinda ka 
fito dashi daga cikin supermarket din ya zama naka. Sai aka samu wani 
saurayi cikin daqiqa daya dinnan ya fito da kayan da kudinsu ya wuce misali 
saboda tsadansu. Da aka tambaye shi ya akayi ya samu damar fito da irin 
wadannan kaya masu makudan kudi sai Yace: “Tun lokacin da aka ba da 
sanarwar wannan garabasa tun lokacin kullun sai na shiga wannan Supermarket ba domin nayi sayayya ba sai don na duba ire – iren kayan da 
keda tsada kuma wadanda za suyi sauqin dauka a ranar gasar”.
ABIN LURA: Babban abin lura acikin wannnan labari shine yadda wannan saurayi ya yi shiri na musamman domin haqarsa ta cimma ruwa, wannan fa wani lamari ne na duniya yayi tattali saboda shi, ina ga wanda ke bidar Aljanna ai min baabi aula yayi shiri domin samunta.
Yau idan akace akwai wani babban bako da zai ziyar ce ka, kakanyi iya yinka wajen shirin yadda za ka tarbe wannan bakon, duk saboda ka dadantawa wannan bakon rai, Kwanaki kadan ya rage babban bako ya ziyarce ka me dauke da rahama da gafara (wato watan Ramadan) shin ko ka yi shiri domin tarbon sa ???
Kafin na shiga kai tsaye kan gun darin jawabin zan so musan wane wata ne watan Ramadan ?
Watan Ramadan shine wata na tara (9) acikin jerangiyar watannin 
musulunchi, wanda yake tsakanin Watan Sha‟aban da Shawwal, kuma shine 
watan da Allah (SWT) ya wajabtawa musulumi azumtar sa.
Mu haÉ—u a fitowa ta gaba 
 *Assalamu alaikum*

Post a Comment (0)