*DA ME ZAMU FUSKANCI RAMADAN??*
*004*
Daga cikin ayyukan da mutum ya kamata ya mayar da hankali kafin zuwan Ramadan Akwai...
👉🏻 *KAMMALA AYUKKA DA ZASU SHAGALTAR*
Magabata sun kasance kafin isowar watan Ramadan sukan yi kokari su kammala duk wani aiki da ze shagaltar su daga bauta, idan kuma aiki ba zai kammala ba kafin Ramadan toh sukan dakatar dashi da zuwan Ramadan saboda su samu damar shagaltu da bautar Allah.
Shi yasa idan muka duba mafi yawa daga cikin Malaman musulunchi sukan rufe majalisan su da zarar Ramadan ya zo domin su shagaltu da karatun Qur‟ani da sauran Ibadu.
👉🏻 *YAWAITA AZUMI A WATAN SHA’ABAN*
Yana daga cikin tanadin zuwan watan Ramadan yawaita Azumi a watan
Sha‟aban kamar yadda Fiyayyen halitta ya kasance yana yi.
Hadisi ya
tabbata acikin Sahihul Bukhari (1969) da Muslim (1156)
Aisha (RA) Tace: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumi har sai munce ba ya ci, kuma yana ci har sai munce ba ya azumi, Ban taba ganin Manzon Allah (SAW) Ya cika azumin wani wata ba sai Ramadan, kuma ban taba ganin watan da yake yawaita azumta ba kamar Sha‟aban.
Hadisi ya tabbata daga Usama dan Zaid (RA) Yace: Nace Ya Manzon Allah (SAW) Banga kana azumtar wani wata ba kamar yadda kake azumtar Sha‟aban, sai Annabi Yace: “Wannan wata ne da mutane suke shagaltuwa gareshi tsakanin Rajab da Ramadan, kuma wata ne da ake daukaka ayukka zuwa
ga ubangijin Halittu, ni kuma ina son a daukaka aikina ina Azumi”
Nasa‟i Ya ruwaito shi (2357) kuma Albani ya ingantashi acikin Silsilatul
Ahadis Assahiha (1898).
*Allah Ubangiji ya Riskar damu watan Ramadan da imani da Lafiya Amin.
*Mu haɗu a Rubutu na gaba*
✍🏻 *Musa Yaqoub Sulaiman (Ibnkhasir* )